Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamna Mai Mala Buni, na jihar Yobe, ya mika motoci 24 da aka gyara ga hukumomin tsaro a jihar domin kara karfinsu na daukar matakan gaggawa kan kalubalen tsaro.
Buni ya yi alkawarin gyara motocin da jami’an tsaro ke da su, a taron tsaron jihar da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Damaturu kwanakin baya.
Taron wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Honarabul Idi Barde Gubana, ya mika motocin ga rundunar ‘yan sandan jihar Yobe da kuma hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA da nufin karfafa ayyukan tsaro a fadin jihar.
A cewarsa, motocin za su taimaka wajen magance barazanar tsaro a kan lokaci tare da kara sanya ido da kuma yin sintiri akai-akai.
Gwamnan ya shawarci hukumar ta NDLEA da su kara himma wajen gudanar da ayyukansu domin kawar da illolin shaye-shayen miyagun kwayoyi, wanda shi ne babban abin da ke haddasa duk wani mugun aiki a cikin al’umma.
Buni ya bayyana jin dadinsa kan namijin kokarin jami’an tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan jihar Yobe.
Shima da yake jawabi a wajen taron, mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam (Rtd) ya bayyana cewa, wannan shiri wani muhimmin mataki ne a yunkurin gwamna Buni na inganta ababen more rayuwa da kuma tabbatar da cewa jihar ta zauna lafiya.
Ya kara da cewa, 18 daga cikin motocin da aka gyara an ware su ne ga rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Yobe, yayin da hukumar NDLEA ta jihar Yobe ta samu guda 4 domin yaki da miyagun laifuka da sha da ta’ammali da miyagun kwayoyi masu sa maye ke haddasawa a jihar.