Ƙungiyar ta ce rikicin da ke faruwa a Ribas bai kai matakin da za a ayyana dokar ta-ɓaci ba.
Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF), ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu da gaggauta janye dakatarwar da ya yi wa Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, Mataimakiyarsa, da ’Yan Majalisar Dokokin jihar.
Da yake magana a madadin ƙungiyar, Farfesa Abubakar Jika Jiddere, ya ce babu wani dalili da ya dace da zai sa shugaban ƙasa ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar.
Ya bayyana cewa, kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi ayyana dokar ta-ɓaci ne kawai a lokuta na matsanancin rikici kamar yaƙin basasa, ko rushewar doka da oda, wanda a cewarsa babu ɗaya daga cikinsu da ya faru a Jihar Ribas.
Haka kuma, sun gargaɗi Gwamnatin Tarayya da kada ta bari irin wannan rikicin siyasa ya tsananta a wasu jihohi kamar Kano, inda ake ci gaba da samun saɓani dangane da masarautar Kano.
Aminya.