Daga Abdullahi Alhassan, Kaduna
A wata hira da ya yi da tashar rediyon Freedom, Honorable Shehu Abubakar, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Magajin Gari a karamar hukumar Birnin Gwari, ya yi raddi kan wasu maganganun tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.
Shehu Abubakar ya caccaki El-Rufai, yana mai bayyana mamakin yadda tsohon gwamnan ya ke amfani da kalmomin batanci, yana kiran ‘yan majalisar Kaduna jahilai, duk da cewa da yawansu sun yi aiki tare da shi a gwamnatinsa.
Ya ce majalisa ta gudanar da aikinta bisa doka, inda ta mika rahotonta ga hukumomin da suka dace, don haka babu dalilin da zai sa El-Rufai ya dinga tayar da jijiyar wuya kan batun.
Dangane da batun bashin da aka ci a lokacin mulkin El-Rufai, Shehu Abubakar ya bayyana cewa akwai basussuka da aka ci ba tare da amincewar majalisa ba, yana mai bayar da misali da bashin biliyan 20 daga Zenith Bank da El-Rufai ya karɓa wata guda kafin barinsa mulki. Ya kalubalanci El-Rufai da ya fito ya nuna takardar amincewar majalisa idan har yana da ita.
Haka kuma, Shehu Abubakar ya karyata ikirarin El-Rufai cewa gwamna Uba Sani bai da cancanta wajen naɗa sabon shugaban hukumar tara kudaden shiga ta jihar, watau KADIRS. Ya tunatar da cewa wanda aka cire, El-Rufai ne ya fara ba shi mukami a gwamnatinsa, don haka, idan har yana cewa ba shi da cancanta, to shi ne ya fara cutar da Kaduna da naɗin marasa kwarewa.
A karshe, Shehu Abubakar ya yi kira ga al’ummar Kaduna da su yi watsi da hayaniyar El-Rufai, su ci gaba da goyon bayan gwamnatin Sanata Uba Sani da ke kan mulki domin ci gaban jihar.