Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiGwamna Zulum Ya Raba Tallafin Naira Biliyan 1 Ga Kananan 'Yan Kasuwa...

Gwamna Zulum Ya Raba Tallafin Naira Biliyan 1 Ga Kananan ‘Yan Kasuwa A Biu, Hawul

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya amince da raba tallafin Naira biliyan daya ga ‘yan kasuwa kusan 9,403 kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa (MSMEs) a kananan hukumomin Biu da Hawul.

Shirin na da nufin bunkasa harkokin kasuwanci na cikin gida, da karfafa tattalin arziki, da kuma rage radadin talauci.

Gwamna Zulum ya  raba kimanin  Naira miliyan 560.3 ga ’yan kasuwa 5,603 a Biu da karamar hukumar Hawul, inda kowanen su aka ba shi Naira 100,000.

Bugu da kari, an raba Naira miliyan 439.7 ga matasa da Magidanta  1,800 da ke yankin Biu da kuma ‘yan kasuwa 2,000 a Hawul.

“Gwamnatina ta kuduri aniyar ci gaba da tallafawa kanana da matsakaitan masana’antu tare da karfafawa matasa,” in ji Gwamna Zulum.

“Muna so mu mai da hankali kan kanana da matsakaitan masana’antu (SMEs) don haɓakar tattalin arziki, samar da ayyukan yi, da tabbatar da cewa matasanmu sun tsunduma cikin samun abin yi mai riba.”

Ya bukaci wadanda suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da tallafin yadda ya kamata sannan ya jaddada cewa kudaden da ya basu na daya daga cikin alƙawarin da ya dauka yayin yakin neman zabensa a karo na biyu.

Gwamna Zulum ya kuma kalubalanci matasa da su bunkasa tunanin kasuwanci tare da ba su tabbacin goyon bayan gwamnatin sa.

Ya kuma umurci hukumar kula da harkokin zuba jari ta jihar Borno (BOSIMP) da ta gano tare da tantance karin matasa 2,000 marasa galihu domin a basu irin wannan tallafin jari nan gaba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments