Daga Hussaini Yero, Funtua
A ranar Lahadi ne 23/2/2025, Masarautar Maskan Katsina ta ziyarci ‘Yan Gidan Masarautar da sukayi Hijira sama da shekaru dari daga garin Maskan zuwa Jihar Kaduna inda sukayi masauki a wani tsibiri da alummar garin ke kiransa Maskawa cikin Karamar Hukumar Lele.
Zayarar ta kasance ne Karkashin Jagorancin Magajin garin Funtua,Eng.Shehu Nuhu da Eng,Isyaku Aliyu Maska.
A jawabin sa Alhaji Ibrahim Umar Masakawa wanda yanzu haka shine uba a Masakawa,Kakansu daya da Muhammad Jaji, ya bayyana cewa,munsamu baki daga fadar mai martaba Sarkin Maskan Katsina Hakimin Funtua domin sada zumuncin fiye da sheka ɗari. sun kawo ziyarar ne domin gano zuri’ar danuwan su wadda ake kira da Muhammad Jaji wato Atiku wadda ya baro Garin Maska ta jihar katsina sabo da rigimar sarauta. Wadda daga karshe ya kafa Garin sama da shekaru dari.
Alhaji Ibrahim Umar Masakawa ya bayyana tarihin iyaye maza da mata da gwagwarmaya da suka sha wajan kafa garin Masakawan.
Akarshe ya bayyana godiyar sa da wannan ziyar karfafa zuminci.kuma yau kunzo gida tamkar kina cikin Garin Maska ne .
Shima a nasa jawabin Jagoran tafiyar Magajin garin Funtuwa,Eng.Shehu Nuhu ya tabbatar da cewa lallai kam sunzo gida da suke da tushen tsakanin kaka da kakanni.kuma munji daddin tarbar da akayi mana da kuma yadda muka karu da tarihin kakannin mu.
Kuma wannan ziyar ta kara mana kywarin gyuwa na nema dangin mu a duk inda suke a fadin kasar nan da wajan ta inji ,Magajin garin Funtuwa.
Mudassir Ibrahim ya bayyana jindadinsa, ganin ashes suna da tushen mai rasa wanda kuma ya wanzu a fadin kasar nan .ya kuma tabbatar da cewa,zasuyi Iya kokarin su a matsayinsu na matasa dan zakulo dangin su a fadin kasar nan.dan kyatata alakar zumunta a tsakanin mu .