Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiJihar Yobe Za Ta Karbi Bakuncin Gwamnonin Tafkin Chadi Karo Na 5

Jihar Yobe Za Ta Karbi Bakuncin Gwamnonin Tafkin Chadi Karo Na 5

Daga, Sani Gazas Chinade.  Damaturu

A kokarin da ake yi na gudanar da taron masu ruwa da tsaki na kungiyar hada kan Jihohi da kasashen yankin tafkin Chadi a wannan karon Jihar Yobe ne  za ta karbi bakuncin kungiyar gwamnonin tafkin Chadi (LCBGF) karo na 5 a cibiyar taron kasa da kasa ta Indimi da ke Maiduguri a jihar Borno, daga ranar 29 zuwa 31 ga watan Janairu, 2025.

Taron wanda hukumar kula da tafkin Chadi (LCBC) tare da hadin gwiwar hukumar tarayyar Afirka (AUC) da hukumar bunkasa ci gaban majalisar dinkin duniya (UNDP) suka shirya, zai mayar da hankali ne a kan taken: “Sake gina yankin tafkin Chadi: karfafa riba, sadaukarwa zuwa yanayin aminci, haɗin kan iyakoki, tsaro da ci gaba mai dorewa don al’umma.”

Da yake jawabi gabanin taron, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana kudirin gwamnatinsa na samun nasarar wannan taro, inda ya bayyana muhimmancinsa wajen samar da hadin kai a yankin da kuma ci gaba mai dorewa a yankin na tafkin Chadi.

“A matsayina na mai masaukin baki na wannan taro na kungiyar gwamnonin, ina matukar farin ciki da sake jaddada aniyar jihar Yobe na ci gaba da hadin gwiwa don samun ci gaba mai dorewa a fadin yankin tafkin Chadi,” in ji Buni.

Taron zai hada mahalarta kusan 500 da suka hada da wakilai daga gwamnatocin kasashen Kamaru, Chadi, Nijar, da Najeriya,  kungiyoyi masu zaman kansu;  CSOs;  shugabannin gargajiya;  da masu ba da taimako, manyan abokai kan aikin fasaha, cibiyoyin bincike, da hukumomin majalisar dinkin duniya wadanda su ma za su shiga cikin tattaunawar.

Ambasada Mamman Nuhu, babban sakataren kungiyar a LCBC kuma shugaban tawagar hadin gwiwar dakarun sojan kasa da kasa da ke yankin na tafkin Chadi (MNJTF), ya bayyana taron a matsayin wani muhimmin dandali na ayyukan jin kai, ci gaba, da zaman lafiya don tsara tsare-tsare masu inganci don daidaita yankin da kuma ci gaba da farfadowar sa.

Ambasada Adeoye Bankole, kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro, hukumar tarayyar Afirka ya ce “wannan kungiyar gwamnonin tafkin Chadi ya kasance muhimmin dandali don inganta ci gaba mai dorewar zaman lafiya da tsaro a yankin.”

Za a gudanar da ayyukan gabanin taron ne daga ranar 27 zuwa 28 ga watan Janairu, inda za a mai da hankali kan hada kai ta hanyar tattaunawa da kungiyoyin farar hula, da shugabannin gargajiya na cikin gida.

Hakazalika tattaunawar za ta ta’allaka ne kan hadin kan al’umma, zaman lafiya, da hana tashin hankali a yankin na tafkin Chadi.

Tun da aka kafa wannan kungiya ta yi matukar taka muhimmiyar rawa dabam-dabam wajen tunkarar kalubale masu sarkakiya da ke fuskantar tafkin Chadi.

A cewar Mista Njoya Tikum, daraktan hukumar UNDP reshen yankin yammacin Afirka ta yamma da tsakiyar Afirka, cibiyar tabbatar da zaman lafiya ta yankin ta samar da ayyuka masu tasiri, kamar gyara gidaje, makarantu, da cibiyoyin kiwon lafiya, tare da ba da damar kusan mutane rabin miliyan ‘yan gudun hijira a cikin gida sun koma cikin  al’ummarsu.

Taron zai tantance irin ci gaban da aka samu ya zuwa yanzu, tare da cimma matsaya kan dabarun inganta hadin gwiwa a yankin, da kuma ba da shawarar sabbin hanyoyin samar da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa.

 

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments