Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
A wani gagarumin mataki na karfafawa mata da ‘yan mata, uwargidan gwamnan jihar Borno, Dakta Falmata Zulum, ta jagoranci yaye dalibai 162 da suka kammala karatu a makarantar koyon sana’o’in hannu da ke Bolori II a Maiduguri bisa kwazo da jajircewar su.
Taron wanda ya gudana a makarantar koyon sana’o’i (skulls Acquisition School) Ngarranam, Bolori II, Maiduguri, gwamnatin jihar Borno ce ta kaddamar da shi a matsayin wani gagarumin mataki na karfafawa mata da ‘yan mata, musamman wadanda ba su yi kasa a gwiwa ba wajen neman ilimi ko kuma ‘yan gudun hijira.
Shirin ya kuma yi nufin bunkasa tattalin arziki a jihar ta hanyar baiwa mata sana’o’i.
Kwamishinan Ilimi, Kimiyya, Fasaha, da Ƙirƙiri na Jiha, injiniya Lawan Abba Wakilbe, ya jaddada cewa shirin ya yi dai-dai da manufar Gwamna Zulum na samar wa jihar Borno hanyar bullewa kan harkokin Kawar da zaman banza da tattalin arziki.
Ya kuma sanar da cewa kowane wanda ya kammala karatunsa zai samu kayan fara aiki da zai taimaka wajen fara sana’o’i don tsayawa da kafafun su.
Makarantar koyon fasaha ta biyu da tsohuwar gwamnatin marigayi Mohammed Goni ta kafa ta bayar da horo kan sana’o’i daban-daban kamar sana’o’in kwamfuta, sana’o’in hannu, sana’ar saka, gyaran fuska, aikin fenti, sana’ar dinki, da yin matashin kai.
Daliban da suka yaye, wadanda da suka samu horon sana’o’i daban-dabam sun baje kolin basirarsu a yayin bikin, inda suka bayyana nasarorin da suka samu.
Goni Ibrahim, babban mai taimakawa gwamna a fannin fasaha a kan TVET, ya jaddada rawar da shirin ke takawa wajen karfafa wa mata da ba su damar bayar da gudumawa mai kyau ga iyalansu da al’ummarsu.
Wakiliyar daliban da aka yaye, Falmata Mohammed, ta bayyana godiyarta ga gwamnatin jihar, da uwargidan gwamnan, da duk wadanda suka taimaka wajen ganin shirin ya samu nasara.
Shugabar kungiyar ‘Multi Aid Charity Initiative’ Hajiya Maryam Gimba, ta ja hankalin daliban da aka yaye da su kula da kansu domin su samu kwarin guiwa, dogaro da kai ta ce, “Wadannan sana’o’in za su ba ku damar zama masu zaman kan ku da kuma ba da gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin jihar mu.”
An kammala taron ne tare da gabatar da takardun shaida da kayan aikin fara aiki ga daliban da suka kammala karatunsu cikin nasara, wanda ya nuna nasarar kammala horar da su na sanin makamar aiki da kuma farkon tafiyarsu na samun ‘yancin cin gashin kai a fannin tattalin arziki.