Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiGwamnatin Yobe Ta Kashe Sama Da N20bn Akan Tituna A Shekarar 2024...

Gwamnatin Yobe Ta Kashe Sama Da N20bn Akan Tituna A Shekarar 2024 –Duddaye

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

Kwamishinan ayyuka na jihar Yobe, Injiniya Umar Wakil Duddaye ya ce ma’aikatar sa ta samu gagarumar nasara wajen samar da muhimman ababen more rayuwa ga al’ummar jihar a shekarar 2024.

Kwamishinan wanda ya yi wa manema labarai karin haske kan nasarorin da ma’aikatar ta samu, ya ce, gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni ta nuna kwazo na musamman ga ci gaban jihar.

Ya zayyana manyan ayyukan da aka kammala a cikin shekarar ta 2024 da suka hada da tagwayen tituna mai tsawon kilomita 25 daga Damaturu zuwa Kalallawa kan kudi naira biliyan 1.6; titin Jajimaji-Karasuwa akan kudi naira biliyan biyu; titin Chumbusko-Tagali mai tsawon kilomita 10 da aka gina kan kudi Naira biliyan 3.3;  da kuma titunan garin Damagum da magudanar ruwa da aka kammala akan kudi naira miliyan 530.

Sauran su ne titin cikin garin Potiskum mai tsawon kilomita 2.6 akan  naira miliyan 582; titin garin Jajimaji da magudanar ruwa akan naira miliyan 788;  da kuma gyara hanyar Biriri-Babbangida da ke kan titin Damaturu zuwa Gashua akan naira miliyan 98.6.

“Akwai kuma gyaran titin Katarko zuwa Goniri, wanda ya hada da gina magudanan ruwa a karamar hukumar Gujba akan kudi N62.8m, gyaran hanyar Buni Yadi zuwa Buni Gari dake karamar hukumar Gujba akan kudi N69. 8m.

“An kuma yi aikin  gadar Kayayya a karamar hukumar Geidam akan kudi N294m;  haka kuma an gina gadar Kayayya ta uku  akan kudi #32,854,054.70.

“Haka nan an gina hanya a rukunin gidajen Bukar Abba Ibrahim Estate da ke garin Potiskum, akan kudi N93m,” in ji shi.

Injiniya  Wakil ya ba da tabbacin cewa za a ci gaba da gudanar da ayyukan da ake ci gaba da yi.

Ya ce wadannan sun hada da gyaran hanyar Geidam zuwa Bukarti akan kudi naira biliyan 1.1, mahadar Kanamma dake karamar hukumar Yunusari akan naira biliyan 2.6, da kuma hanyar Nguru zuwa Balanguwa akan naira biliyan daya.

Sauran sun hada da hanyar Gashua zuwa Masaba mai tsawon kilomita 25.5 akan kudi naira biliyan 4.4;  Titin Fika-Maluri mai tsawon kilomita 22.5 a karamar hukumar Fika akan kudi Naira biliyan 2.2;  da hanyar Kukuri-Chukuriwa-Dawasa a karamar hukumar Nangere akan kudi Naira biliyan 1.2.

Kwamishinan ya zayyana sauran ayyukan da ake gudanarwa da suka hada da kofar shiga birnin Damaturu da aka bayar kan kudi naira miliyan 860,  gina tituna ma su nisan kilomita  4.2km da magudanar ruwa mai tsawon kilomita 8.4 a Potiskum kan kudi naira biliyan 1.1, da karin titin kilomita 4 daga babbar hanyar Nguru zuwa Karasuwa da sauran ayyuka.

Kwamishinan ya kuma bada tabbacin kammala dukkan wasu ayyukan da suka fara nan da karamin lokaci in Allah SWT ya so.

 

 

 

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments