Daga Hussaini Yero
Matsalar Tsaro a Zamfara,karamin Minista Bello Matawale yayiwa Jihar Zamfara dirar mikiya Inda zai ziyarci garuruwan da matsalar tsaro taking ci taki karewa a ziyarsa ta kwana biyar a Jihar.
Ministan Matawale a taron magoya bayan Jami’yya APC da sukai dandazo a gidansa da ke Gusau,ya bayyana cewa,yazo ziyarar aiki ne kwana biyar kamar yadda yayi a Sokoto a kwannan baya kuma zanzagaya duk Inda ke da matsalar tsaro dan kawo karshen “Yan ta’adda da suka addabi mu.
Kuma wannan yana daga cikin kudirin Shugaban Kasa Bola Ahmad Tunibo na samar da jiragen yaki na zamani da makamai dan kawo karshen “Yan Bindiga a shekara ta 2025.Inji Matawale”.
Matawale ya tabbatar da cewa,duk wani mai taimawa “yan Bindiga a Dajie ko gari ya kuka da kansa.akan haka ne Ministan Matawale yayi kara da babbar murya cewa,da taimakon mutane na rahotan siri ga Jami’an tsaro zai taimaka mana wajan cimma burinmu na yaki da ‘yan Bindiga.