Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiNEDC Ta Gudanar Da Bita Ga 'Yan Jarida Da Kungiyoyin Sakai A...

NEDC Ta Gudanar Da Bita Ga ‘Yan Jarida Da Kungiyoyin Sakai A Arewa Maso Gabas

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

Hukumar raya yankunan Arewa maso Gabas (NEDC) tare da hadin gwiwar kamfanin tuntuba na (Ranlal Global Services) sun fara gudanar da wani taron bita/ horaswa na kwanaki uku kan inganta kafafen yada labarai da kungiyoyin farar hula (CSOs) kan hanyoyin da ba su dace ba na yaki da ta’addanci a yankin.

Wakilinmu ya ruwaito cewa horon a cewar hukumar NEDC an shirya  shi ne domin karfafawa ‘yan jarida da kungiyoyin fararen hula (CSO) ilimin da ya dace kan yadda za su ba da gudummawa wajen samar da zaman lafiya a yankin na arewa maso gabas da ke fama da rikicin ‘yan tada kayar baya.

A nasa jawabin a yayin bude taron bitar babban manajan darakta kuma shugaban hukumar NEDC Muhammad Goni Alkali Wanda wani jami’in hukumar  Mohammed Sani Umar ya wakilta,  ya ce taron horaswar zai karfafa gwiwar rawar da hukumar zata taka da kuma kafofin watsa labaru na inganta alƙawarin da za’a dauka don haifar da ci gaba mai dorewa a yankin
musamman a wannan  yankin mai matukar  mahimmanci na arewa maso gabas.

Haka nan an tsara wannan horon ga ‘yan jarida da nufin koyar da su yadda za su yi amfani da kayan aiki da za’a samar musu don cigaba da gudanar da ayyukan su da zimmar  magance ƙalubale na musamman na bayar da rahoto a wannan yanki.

“Ayyukan ku na ’yan jarida na da muhimmanci wajen haskaka gaskiyar lamari  da ke iya zaburar da al’umma da kuma abubuwan da suka shafi tsaro a wannan yanki na arewa maso gabas.”

A cewar sa akasari akan bi hanyoyin amfani da karfin soja ne wajen lalubo bakin zaren kawo karshen wannan matsala maimakon yin amfani da karin wasu hanyoyin da suka hada da hanyar lallami da zama akan teburin shawarwari da makamantan su.

“Wannan horon ya hada ‘yan jarida 100 da kungiyoyin fararen hula (CSO) daga jihohi shida na shiyyar Arewa maso gabas domin sanin hanyoyin bi don kawo karshen rikicin na masu tada kayar baya.”

“Yankin arewa maso gabashin Najeriya ya sha fama da tashe-tashen hankula, wanda ya haifar da rikice-rikicen jin kai, da barnar matsugunai, da  barnar tattalin arziki.”

Farfesa Umar Pate na Jami’ar gwamnatin tarayya da ke Kashere ne ya gabatar da makaloli a ranar farko akan harkokin watsa labarai da tasirin manufofi da dabarun binciken aikin Jarida don kwantar da rikici, matsayin kafofin yada kabarai a wajen yin sulhu da sake haɗin kai, yayin da fahimtar take-taken masu tada kaya kan hakan.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments