Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce gwamnatinsa ta mayar da yara sama da miliyan 1.5 zuwa makaranta.
Adadin ya nuna kashi 70% na yara miliyan 2.2 da ba sa zuwa makaranta a dukkan fadin jihar ta Borno.
Gwamna Zulum ya bayyana haka ne a ranar Talata a lokacin kaddamar da Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Mairi da Daraktan Bankin Duniya, Dr. Ndiame Diop ya yi.
Ya ce, a cikin shekaru biyar da suka gabata, gwamnatin ta dauki nauyin saka Kara habaka fannin ilimi ta wajen mayar da yaran ya zuwa makarantu inda ya ce sauran yara 700,000 za a saka su a makarantu nan ba da dadewa ba da izinin Allah SWT.
“Mun gina makarantu kimanin 104, mun gyara ajujuwa 2,931, tare da raba kayayyakin ilimi kyauta, wadanda suka hada da littafan rubutu miliyan 20, litattafan karatu miliyan 2, uniform miliyan 15 na kayan makaranta, jakunkunan makaranta 700,000, da kuma miliyoyin kayayyakin koyo,” in ji gwamnan.
Ya kara da cewa shirin ciyar da daliban ya amfana da dalibai 50,000 a jihar, yayin da gwamnati ta kuma samar da kekuna 10,000 ga dalibai a yankunan karkara domin saukaka kalubalen sufuri.
Gwamna Zulum ya ce, wajen magance matsalar matasan da ba su zuwa makaranta da suka wuce shekarun karatu na al’ada, gwamnatin ta ba da fifiko kan ilimin fasaha da koyar da sana’o’i (TVET).
“Mun kafa Cibiyoyin Sana’o’i guda biyar, Makarantun Sana’o’i na Mata/Yan Mata biyu, sannan mun sake farfado da Cibiyoyin Koyar da Sana’o’i guda tara.
“Manufarmu ita ce horar da masu sana’a kusan 5,000 a duk shekara, tare da ba su karfin gwiwa don dogaro da kai da magance kalubalen rashin aikin yi.”
A nasa jawabin, Daraktan Bankin Duniya Dr Diop ya yaba da kudurin jihar Borno na sake gina fannin ilimi, inda ya bayyana cewa bankin ya tallafawa gina makarantun sakandire 41 da kuma gyara makarantu 392 a fadin jihar.
“Wannan makaranta alama ce ta kokarin gwamnatin Borno wajen sake ginawa duk da halin rashin tsaron da aka yi fama da shi Kokarin da jihar ke yi ya burge mu kuma za mu ci gaba da tallafa wa manufofin Gwamna Zulum,” in ji Diop.