Daga, Sani Gazas Chinade , Damaturu
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2025, mai taken “kasafin farfadowa da ci gaba,” tare da jimillar kudi naira biliyan ₦584.76 da nufin karfafa ci gaban jihar.
A cikin sanarwar da Comred Dauda Iliya, kakakin gwamnan ya fitar, ya ce kasafin ya fi ba da fifiko kan harkokin kiwon lafiya, ilimi, da farfado da tattalin arziki, tare da saka hannun jari mai muhimmanci a fannin tsaro, samar da ababen more rayuwa, da ayyukan jin kai.
Kasafin kudin ya kunshi kashe Naira Biliyan 380.84 na harkokin yau da kullum da kasafta kudi na Naira Biliyan 203.92 da za’a samar da shi ne ta daga kudaden da ake iya samu daga gwamnatin tarayya (FAAC) sai naira ₦ 311.70 biliyan, daga harajin cikin gida(IGR) da ₦ 30.09 biliyan, da karin ₦ 237.96, wanda ya hada da taimako, tallafi, da kuma bunkasa jari.
Gwamna Zulum da yake sanar da rabon bangaren, ya ce bangaren lafiya shi ne ya samu rabo Mai tsoka na Naira biliyan 89.97 wanda ya zo dai-dai da kashi 15.39% na adadin kasafin kudin.
Ya sanar da tsarin kiwon lafiya mai karfi, wanda ya hada da, gina asibitin kashi a Maiduguri, kafa manyan asibitoci a garuruwan Magumeri, Gubio, Azare, Uba, Dikwa, Kaleri, da Mafa, tare da gyara asibitocin Baga da Mulai.
Za Kuma a kammala tare da kaddamar da asibitin koyarwa na Jami’ar Jihar Borno da ke Maiduguri da kuma fadada tsarin inshorar lafiya na jihar ga ma’aikatan gwamnati da marasa galihu a fadin kananan hukumomin 27 na Jihar.
“Samar da ma’aikatan gwamnati cikin Tsarin Inshorar lafiya ta Jiha, sannan a fadada shigar da ‘yan Jiha masu kananan karfi a fadin kananan hukumomi 27 cikin asusun samar da lafiya na asali”.
Zulum ya kara da cewa, “Hukumar bunkasa kiwon lafiya matakin farko ta jihar Borno za ta farfado da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda 100 a jihar tare da shirin gina karin cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda 6 da kuma inganta 6 PHC zuwa manyan cibiyoyin kiwon lafiya”.
A bangaren ilimi wanda an ware kimanin naira biliyan 69.81, Gwamna Zulum ya bayyana cewa shirin samar zai samar da sabuwar makarantar zamani (Chance) ta biyu, gina karin makarantun na musamman Mega guda biyar da manyan makarantun islamiyya na Mega biyar, gyara wasu makarantu da kayan aiki a makarantu 50 dake fadin jihar.
A bangaren harkokin tsaro, bada tallafi, samar da aikin yi ga matasa, gwamnan ya samar da kasafi mai Kauri don Inganta rayuwar al’ummar Jihar.