Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamnatin Jihar Borno na Shirye-shiryen gina layukan dogo na farko a arewacin Najeriya a babban birnin Jihar Maiduguri don saukakawa al’umma wajen harkokin zirga-zirga a birnin.
Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin Kwamishinan Sufuri da Makamashi na Jihar Alhaji Mohammad Bamanga, yadda ya ce an tsara tare da shirya wannan gagarumin aikin ne domin inganta harkokin sufuri, da bunkasa harkokin tattalin arziki, da kuma samar da ci gaba mai dorewa a birane.
Alhaji Bamanga ya ce aikin layin dogo zai kunshi tashoshi 12 da aka kebe wadanda za su hada manyan kasuwanni, makarantu, da wuraren taruwar jama’a, da kuma wurare masu muhimmanci ga tattalin arziki a birnin na Maiduguri.
A cewarsa, wannan shiri ya kasance irinsa na farko da kowace jiha daga cikin jihohin Arewa 19 za su yi, tare da shirin fadada wasu kananan hukumomi a nan gaba.
Yayin da yake duba tashoshin jiragen kasa da aka tsara da kuma hanyoyin da aka tsara tare da Kamfanin da zai gudanar da aikin 18, EEC, Kwamishinan ya ce, ana ci gaba da gudanar da nazarin yuwuwar, tantance hadarin muhalli, da tuntubar al’umma kafin fara aikin gadan-gadan.
“Wadannan matakai an yi niyya duba su ne don tabbatar da an aiwatar da aikin cikin nasara ba tare da kawo cikas ga muhallin al’ummomin yankunan da aikin zai ratsa ta wuraren su.”
“Aikin hanyoyin jirgin kasa zai canza hanyoyin sufuri na birni ta hanyar sauÆ™aÆ™awa al’umma ta hanyar farfado da tattalin arziki, samar da ayyukan yi, da buÉ—e hanyoyin Inganta tattalin arziki al’umma matuka.”
Ya ce, matakin farko na layin dogo an tsara shi ne don karawa wasu ayyukan samar da ababen more rayuwa da ake yi, wadanda suka hada da fadada hanyoyin Maiduguri mai nisan kilomita 113 na Gabas, Yamma, da Kudu wadanda suka hada muhimman al’ummomi kamar na Auno, Molai, Polo, da rukunin gidajen Shagari wato shagari kwatas.
Alhaji Bamanga ya ce aikin layin dogo wani bangare ne na dabarun sabunta biranen Jihar da gwamna Babagana Zulum ke da kudirin aiwatar da su.
Ya ce jihar ta kuma bullo da motocin bas masu amfani da wutar lantarki da iskar gas da kuma motocin haya, wanda aka ba su a farashi mai rahusa don rage tasirin cire tallafin man fetur ga mazauna yankin.