Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da jihohi biyar sun karfafa tsarin kiwon lafiyar su tare da ba da agajin gaggawa a arewa maso gabas da wasu Jihohin da ke tsakiyar Najeriya.
A cewar kungiyar, fannin kiwon lafiya a yankin na arewa maso gabas yanki ne da ya fuskanci kalubale masu tsanani, da suka hada da lalata kayayyakin more rayuwa da kuma raba jama’a da matsugunin su tare da kara samun barkewar cututtuka.
Wakilin hukumar lafiya ta duniya, Dr. Walter Kazadi Mulombo, ne ya bayyana hakan a Maiduguri, a wani taron hadin gwiwa karo na 14 kan agajin jin kai tsari na 3 a jihohin Borno, Adamawa, da Yobe.
Ya ce sake duba tsarin bayar da kiwon lafiya shi ne don inganta sakamakon kiwon lafiya a jihohin da ake fama da rikici da ambaliyar ruwa, ciki har da jihohin Benue da Filato da ke arewa ta tsakiya.
“A cewar sa tun daga shekarar 2016, harkokin jin kai ya taso a yankin arewa maso gabas, wanda rikicin Boko Haram ya haddasa, ya jawo wahalhalu da hargitsi daban-dabam.”
“Bugu da kari, ya lura cewa bangaren kiwon lafiya ya fuskanci kalubale masu tsanani, da suka hada da lalata ababen more rayuwa, da kauracewa jama’a, da kuma kare hadarin barkewar cututtuka kamar yadda na ambata a baya.”
Duk da wadannan matsaloli, Mulombo ya bayyana cewa, kokarin hadin gwiwa na hukumar lafiya ta duniya da jihohi sun samar da muhimman ayyukan kiwon lafiya, ta yadda suka nuna juriya da jajircewa.
Dangane da kalubalen da ake fuskanta a fannin kiwon lafiya, ya ce: “Bari bayyana irin barnar da ambaliyar ruwa ta yi a Maiduguri, Jere, Mafa, da Maiduguri Metropolitan Council (MMC) da cewar abin dubawa ne.
Ya koka da cewa hakan ya kara ta’azzara kalubalen da ake fuskanta a fannin kiwon lafiya, da suka hada da raba mazauna yankin kusan miliyan daya, galibi mata da kananan yara da muhallin su.
Dangane muhimman abubuwan da suka faru a fannin kiwon lafiya kuwa, Mulombo ya ce, “Akwai gagarumin aikin kula da lafiya na gaggawa da kuma gangamin rigakafi,” yana mai cewa sun kuma karfafa tsarin kiwon lafiya da matakan gaggawa na jihohin biyar.
A cewarsa, jihohin biyar sun jaddada muhimmancin koyo daga wadannan abubuwa da suka faru domin bunkasa dabarun daukar matakan gaggawa.