Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya jaddada kudirin gwamnatinsa na sake tsugunar da wadanda rikicin Boko Haram ya shafa cikin mutunci da tsari mai dorewa.
Gwamnan ya yi wannan alkawarin ne a yayin ziyarar ban girma da ministan harkokin jin kai da yaki da fatara, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, ya kai masa ranar Talata a fadar gwamnati dake Maiduguri.
Da yake jawabi a ci gaba da kalubalan da ‘yan gudun hijirar ke fuskanta, Gwamna Zulum ya jaddada cewa tallafin da kungiyoyi na kara tsukewa, shi yasa akwai bukatan tsugunar da jama’a maikokon cigaba da zama a sansanonin ‘yan gudun hijira.
“Masu gudun hijira sun dade da yawa a sansanonin; Muna son su tashi su sami abin rayuwarsu. Yayin da kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyi masu zaman kansu suna aiki abin yabawa, babu wani ci gaba da bayar da kudade don ciyar da mutane a wadannan sansanonin,” in ji Zulum.
Gwamnan ya jaddada bukatar samar da tsari mai dorewa don magance kalubalen jin kai da suka hada da sake tsugunar da mutanen da suka rasa matsugunansu.
Ya yi alkawarin hada kai da hukumomi da ke karkashin ma’aikatar jin kai don gaggauta dawo da ‘yan gudun hijirar cikin aminci da mutunci.
A jawabin sa, Ministan Harkokin Agaji, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, ya sanar da shirye-shiryen ma’aikatar don sanya tsarin jin kai na Borno cikin cikakken Tsarin Ba da Agajin Gaggawa na kasa.
Ya yabawa Gwamna Zulum kan yadda ya mayar da hankali wajen dawo da gyare-gyare, da kokarin sake ginawa, wadanda suka kasance masu muhimmanci wajen dawo da ababen more rayuwa da kuma farfado da rayuwar al’umma a jihar.
“Gwamna Zulum ya bayar da jagoranci na kwarai ta hanyar daidaita kokarin jihar da abokan huldar kasa da kasa, tare da tabbatar da cewa a hankali ayyukan rayuwa da zamantakewa suna komawa Borno,” in ji Ministan.
Ministan ya kuma bayyana shirin mayar da ‘yan gudun hijirar Najeriya zuwa garuruwan su, tare da yin alkawarin ba su damar dogaro da kai.
Ministan ya samu rakiyar kwamishinan tarayya, hukumar kula da ‘yan gudun hijira, da bakin haure, Hon. Tijani Aliyu Ahmed, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan shirin ciyar da dalibai, Dr. Yetunde Adeniji, tare da manyan jami’an ma’aikatar.
Dauda Iliya
Mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Borno
(Kan yada labarai/Mai magana da yawun sa)