Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Hukumar Hisbah ta jihar Yobe ta lalata kwalaben barasa sama da 170 wanda kudinsu ya kai kimanin N450,000.
Kamar yadda rahoton ke nunawa hukumar ta Hisbah ta kwace kwalaben barasar ne a daya daga cikin otal da ke garin Gashua, hedikwatar karamar hukumar Bade.
Shugaban karamar hukumar Bade, Alhaji Ibrahim Babagana Yurema, wanda ya jagoranci barnata barasar ya ce majalisar za ta fatattaki masu siyar da barasa da masu shaye-shaye a yankin.
Ya ce an kwace kwalaben ne a yayin wani sintiri da hukumar Hisbah ta yi a daya daga cikin fitattun otal-otal da ke garin na Gashuwa, inda ya ce majalisar ta karamar hukumar ta damu da shaye-shaye a tsakanin matasan yankin.
Shugaban ya Kara da cewar, shan barasa da sauran abubuwan sa maye da ke gurbata tunanin mutum haramun ne a addinin musulunci, yana mai jaddada cewa majalisar za ta ci gaba da yaki da wannan mummunar dabi’a a tsakanin matasan yankin.
Don haka ne shugaban ya gargadi matasan da su kaucewa shiga wannan irin mummunar halayyavta shaye-shaye kayayyakin sa maye wadda a karshe babu abin da ke haifarwa face shiga halin bacewar hankalin da aikata ta’assa.
A jawabin sa Kwamandan hukumar Hisbah na shiyyar Yobe ta Arewa, Malam Isah Ibrahim, ya ce kotun shari’ar musulunci a jihar ta samu wanda ya ke siyar da barasar da laifi, inda ya ce kotun ta kuma umarci hukumar Hisbah da ta lalata barasar da aka kwace ba tare da wani jinkiri ba.