Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiKotun Tarayya dake Kano ta rushe shuganancin hukumar zabe ta Jihar

Kotun Tarayya dake Kano ta rushe shuganancin hukumar zabe ta Jihar

Daga Rabiu Sanusi

Wata Kotun Tarayya dake zaman ta a jihar Kano ta umarci jami’an tsaro da su ƙauracewa zaben ƙananan hukumomin da za’a gudanar a KanoPublished 3 mins ago on 22/10/2024 By Hassan Mamuda Ya’u

Babbar kotun mai zamanta a Kano karkashin jagorancin mai Shari’a Simon Amobeda, ta rushe shugabancin hukumar zabe ta jahar Kano Kanseic.

Kotun dai ta ɗauki wannan mataki ne bisa dogaro da hujjojin da áká gabatar mata na rashin cancantarsu, kasancewarsu ƴan Siyasa kuma suna ɗauke da katin Jam’iyyar NNPP.

Cikin wata kara wadda Aminu Aliyu Tiga da Jam’iyyar APC suka shigar suna rokon kotun da ta rushe su.

Kotun ta kuma umarci jami’án tsaro da su ƙauracewa zaben ƙananan hukumomin da za’a gudanar tare da umartar hukumar zabe ta kasa INEC, da kada ta bayar da kayan zaben.

A ranar Asabar ne dai 26 ga watan Oktoban 2024, za’a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar Kano.

idan dai za’a iya tunawa zaben kanan hukumomi da za’a gudanar a jihar kano bai wuce Qasa da kwanaki kadan ya rage a gudanar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments