Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeSiyasaNNPP ta dakatar da Baffa Bichi Kano da wani Kwamishinan Sufuri

NNPP ta dakatar da Baffa Bichi Kano da wani Kwamishinan Sufuri

….Ko ina Gizo ke sakar?….

Daga Rabiu Sanusi

Jam’iyyar NNPP ta jihar Kano ta bayyana dakatar da sakataren gwamnatin jihar Dakta Abdullahi Baffa Bichi, da Kwamishinan Sufuri na jihar Kano Muhammad Diggwal, daga cikin jam’iyyar.

Shugaban jam’iyyar NNPP a Kano Dakta Hashim Sulaiman Dungurawa ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da aka aikowa Dala FM Kano, a cikin daren yau Litinin.

Hashim Dungurawa, ya ce dakatar da ƙusoshin gwamnatin jihar Kanon su biyu,ya biyo bayan zargin keta alfarmar jagoranci, da ta Jam’iyya, da kuma keta alfarmar gwamnati, a don haka ne suka ɗauki matakin ba tare da yin wasa ba akai.

“Jagorancin shugabancin jam’iyyar mu na ƙananan hukumomin da mutane biyun suka fito sun gabatar mana da ƙorafe-ƙorafe kan ƙusoshin gwamnatin biyu, akan zarge-zarge da ake musu ya sa muka ɗauki matakin dakatar da su, har sai mun gama bincike, “in ji Dungurawa”.

Sulaiman ya ƙara da cewar dakatar da Abdullahi Baffa Bichi da Muhammad Diggwal ta fara aiki ne daga ranar Litinin 14 ga watan Oktoban 2024, kamar yadda jam’iyyar ta samu ingantattun shawarwari akan zargin da ake musu.

A wani jawabin kuma sakataren gwamnatin jihar Kano Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya barranta kansa da wata kungiyar magoya baya dake ikirarin yana da hannu wajen batutuwa dake yawo a kafafen sada zumunta na zamani da ake cema ”ABBA TSAYA DA KAFARKA”.

Baffa Bichi yace babu wata kungiya da yake da hannu ciki makamanciyar hakan dan haka bashi da wata alaka da ita.

Sakataren gwamnatin yace idan banda Kungiyar (One to Tell Tell) da yake da yayi kamfen din shugaban Kasa a fadin jihohin Arewa 19 da ake dasu.

”muna yima gwamna biyayya matuka da Jagoran mu na darikar Kwankwasiyya na duniya Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso bisa haka ni bani da wata masaniyya kan wancan batun wata Kungiya da ake alakantata dani.

DAN TAKARAR KUJERAR SHUGABANCIN BICHI A NNPP:

a nasa jawabin dan takarar kujerar Jam’iyyar NNPP na karamar hukumar ta Bichi Hon Hamza Sule mai Fata yace a tsakanin su da Baffa Bichi babu wata matsala.

Hon Hamza Mai Fata ya bayyana haka ne yayin kammala wani zaman rufe kofa daya gudana da gwamna Abba Kabir da Sakataren Gwamnatin da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano harma da sauran masu ruwa da tsaki.

”Mu masu biyayya ne ga Jam’iyyar mu ta NNPP da tafiyar Kwankwasiyya dan haka daga yau bazan kara rike wannan a matsayin wani abu daban ba.

”Gaskiya mungodewa mai girma gwamnan mu bisa jajircewar sa wajen hada kan magoya bayan mu.

wakilin mu ya ruwaito cewa wannan wuta dai nada alaka da hana dan takarar shugaban karamar hukuma da ya fito daga tsagin shi yasa wutar wannan lamari takara ruruwa.

sai dai ba tun yauba ana ganin irin hakan zata kara ruruwa idan har ba’a dauki matakin gaggawa ba to lallai wankin hula zai kawo tsalen badake a wannan Jam’iyyar
NNPP.

Haka kuma a wata majiyar an ce Jam’iyyar ta NNPP ta dakatar na kwamiahinan Sufuri na jihar Kano Hon Muhammad Digol bisa dalilin raahin kame baki daga sakin magana da rashin nuna biyayya ga uwar Jam’iyya ta jihar Kano.

yazuwa yanzu dai dukkan Kallo ya koma sama sakamakon dakatar da manyan Fulogan da ake kallon karan su yakai tsaiko a wannan Jam’iyya da shugabancin ta yasamu damar dakatar dasu a tafiya,yayin da babbar Jam’iyyar adawa watau APC take zawarci dayawan su.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments