Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLafiyaAn  Sake Samun Sabbin Masu Dauke Da Cutar Shan Inna Guda 4,...

An  Sake Samun Sabbin Masu Dauke Da Cutar Shan Inna Guda 4, Bayan Shekaru 3 Da Aka Tabbatar Babu Ita A Yobe

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

An samu sabbin mutane hudu da suka kamu da cutar shan inna a kananan hukumomi uku (LGAs),a Jihar Yobe shekaru uku bayan da aka ayyana jihar ba ta da cutar shan inna.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin babban sakataren hukumar lafiya a matakin farko na jihar, Dakta Babagana Kundi-Machina a lokacin da yake kaddamar da yaki da cutar a garin Machina dake iyaka da jamhuriyar Nijar.

Kundi-Machina ya ce, “Abin takaici ne cewa bayan shekaru uku da aka tabbatar da cewa ba su da cutar shan inna, sai kuma a yanzu muka samu rahoton bullar cutar shan-inna a kananan hukumomin Bursari, Machina, da Yusufari.”

Ya ce gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar abokan huldar ta na cikin gida da na kasa da kasa, sun kaddamar da shirin bayar da rigakafin bullar cutar a fadin jihar domin shawo kan lamarin cikin hanzari.

Ko’odinetan hukumar lafiya ta duniya (WHO) na jihar, Dr Hamisu Alhassan, ya yi alkawarin bayar da goyon bayan hukumar ga jihar domin dakile barkewar cutar akan lokaci.

Alhassan ya bukaci al’umma da su dauki matakan kariya da suka hada da tsaftar mutune, muhalli, wanke hannu da alluran rigakafi domin bunkasa rigakafin da kuma inganta lafiya musamman mata da kananan yara.

A nasa jawabin yayin Kaddamar da Shirin rigakafin Cutar ta Shan innaai Martaba Sarkin Machina, Alhaji Bashir Machinama, ya shawarci al’ummarsa da su baiwa gwamnati hadin kai ta hanyar karbar allurar rigakafin.

Machinama ya godewa gwamnatin jihar bisa gaugawar daukar matakin da ta dauka, ya kuma yi alkawarin wayar da kan al’ummarsa kan daukar matakan da suka dace don dakile cutar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments