Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
A kokarin da ya ke na sace wasu kayan wutar lantarkin daga daya daga cikin na’urorin bada hasken wutar (Transformer) wani mutum da ake kyautata zaton barawon ne, ya gamu da ajalinsa akan wani turken wutar lantarki a rukunin gidajen kwamishinoni da ke garin Damaturu fadar jihar Yobe a zargin da ake yi akan ya na kokarin sace wasu kayayyaki ne daga cikin wata na’urar raba hasken wutar lantarki.
kamar yadda rahoton ya nuna wannan barawon kayan wutar lantarkin ya hau daya daga cikin turakun da ke dauke da na’urar nan ne ta rarraba hanyoyin wutar lantarki (transformer) wanda ake zargin a lokacin da ya hau turken ba tare da sani ba ashe kamfanin bada hasken wutar lantarkin na YEDC ya dawo da wutar kasancewar a lokacin da ya ke kokarin hawa don aikata barnar a sanin sa babu wuta an dauke, to shine fa mai faruwa ta faru.
Blessing Tunoh, babbar, jami’ar sadarwa ta kamfanin rarraba hasken wutar lantarki ta Yola YEDC ne, ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar.
Madam Tunoh ta ce manajan yankin na kamfanin, Operations, ya ziyarci wurin tare da jami’in da ke kula da yankin, bayan samun rahoton faruwar lamarin.
Ta ce, tawagar ‘yan sandan Operation Haba Maza da ke sintiri a Damaturu ne suka fitar da gawar wanda ake zargin daga wannan wuri yadda suka dauki gawar ya zuwa asibitin koyarwa na Damaturu.
Kakakin kamfanin na YEDC ya ce da jin hakan ‘yan uwan mamacin suka zo tare da tabbatar da gawar dan uwan su ne a lokacin da suka isa asibitin. In ji Tunoh.
“Bincike ya nuna cewa marigayin ya yi yunkurin yin amfani da rigarsa wajen kare kansa a lokacin da yake yin ta’ammali da wata waya mai dauke da wutar lantarki jikinta a lokacin da ya ke kokarin aikata wannan aika-aika.
DSP Dungus Abdulkarim, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, ya tabbatar da cewar, marigayin ya yi yunkurin sace kadarorin wutar lantarkin ne da misalin karfe 1:00 na dare yayin da hakan ta faru.
“A cewar sa a lokaci akwai matsalar wutar lantarki a lokacin da wanda ake zargin ya yi yunkurin aikata da ya shiga tashar da na’urar rarraba hasken wutar lantarkin ta ke, amma kwatsam sai wutar lantarki ta kama shi ya gamu da ajalinsa nan ta ke.
“Da asubahin ne mazauna rukunin gidajen suka gano gawarsa a kan hanyarsu ta zuwa masallaci domin yin sallar asuba.
“Ba tare da bata lokaci ba aka kai rahoton lamarin ga sashen Maisandari ‘B’ na rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, inda aka tura jami’ai domin kwashe gawar.
“Za mu ci gaba da tallafa wa hukumar ta YEDC wajen kare gine-ginene, na’urorin su da kuma gurfanar da barayin da aka kama wadanda ke lalata ababen wutar lantarki..in ji ASP Dungus.