Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiHukumar NEDC Ta Tallafawa Al'ummar Da Harin Mafa  Ya Shafa Da Kayan...

Hukumar NEDC Ta Tallafawa Al’ummar Da Harin Mafa  Ya Shafa Da Kayan Masarufi

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Hukumar raya yankin Arewa maso Gabas ta bayar da tallafi mai muhimmanci ga wadanda hare-haren ‘yan ta’addan Boko Haram ya rutsa da su a Mafa da kuma wadanda a ambaliyar ruwa ta shafa a wasu yankunan Jihar Yobe.

Kan abin da ya shafi  ambaliyar ruwa hukumar ta NEDC ta bada tallafi ga wasu mutanen a Nannawaji a karamar hukumar Gujba, wasu mutanen Nguru da  Nangere, sai mutanen Kaliyari da Jumbam a karamar hukumar Tarmuwa da kuma wadanda kisan gillar da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi a baya-bayan nan a garin Mafa cikin  Tarmuwa.

Tallafin da hukumar ta bayar na kayan abinci da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum da suka hada da barguna, zannuwa da kuma dinkakkun tufafi na maza da nufin rage radadin da al’ummar da abin ya shafa ke ciki.

A nasa jawabin, babban shugaban hukumar ta NEDC na kasa Mohammed Goni Alkali, wanda kodinetan Jihar Yobe, Farfesa Ali Ibrahim Abbas ya wakilta, ya jajanta wa gwamnatin jihar Yobe da al’ummomin da wannan lamari ya shafa.

Ga kowace al’ummar da abin ya shafa, kayayyakin da aka bayar sun hada da buhunan shinkafa 200 (25 kg) katan na  Macaroni guda 200, tabarmai guda 200, barguna 200, dinkakkun yadukan shadda guda 200, da kayayyakin kananan yara 200 na sawa da sauran su.

Wadannan muhimman kayayyaki a cewarsa, za su taimaka wajen magance bukatun mutanen da suka rasa matsugunansu da kuma wadanda suka jikkata.

“Gaba ɗaya, don wannan shiri na musamman, an mika wa masu ruwa da tsaki buhunan  1,200 (kg 25), katan 1,200 na Macaroni da tabarmai 1,200 , sai barguna  1,200 barguna, 1,200 da dinkakkun kayan sawa  shadda.guda 1,200.

“Sauran sun hada da zannuwan mata  guda 1,200 da sutirun Yara kanana guda 1,200 na yara”.

“Gudunmawar NEDC shaida ce ta jajircewarta na tallafawa al’umma masu rauni a yankin a arewa maso gabas.”

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments