Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiKisan Gillar Mafa: Ganduje Ya Kai Ziyara Damaturu, Don Jajantawa Gwamnatin Jihar,...

Kisan Gillar Mafa: Ganduje Ya Kai Ziyara Damaturu, Don Jajantawa Gwamnatin Jihar, Al’ummar Yobe

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su karfafa hadin-gwiwa da ake da su domin yaki da ta’addanci da ‘yan fashi da makami a kasar nan.

Shugaban Jam’iyyar APC ya yi wannan kiran ne a Damaturu, yayin da yake jagorantar kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na jam’iyyar domin jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar Yobe kan harin da ‘yan Boko Haram suka kai kauyen Mafa da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Ganduje ya ce Jam’iyyar ta APC  ta je jihar ne domin ta gana da gwamnati da al’ummar jihar a wannan lokaci da aka kai hare-haren wuce gona da iri da kuma kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Ya ce: “Muna tare da al’ummar Yobe, muna jin zafi da bakin ciki dangane da irin wannan abin Allah wadarai da al’ummar jihar Yobe suka fuskanta, wadda don haka ne muka zo don jajantawa ‘yan uwanmu kan wannan mummunan lamari.”

Ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su karfafa hadin gwiwa da ake da shi domin yakar wannan barazana yadda ya kamata.

Ya jajanta wa iyalan wadanda abin ya shafa, tare da bayyana kwarin gwiwar cewa nan ba da dadewa ba jihar za ta fita daga cikinta da yardar Allah.

Da ya ke maraba da wannan babbar tawaga ta uwar Jam’iyyar APC karkashin jagorancin shugaban ta na kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan jihar Yobe, Hon.  Mai Mala Buni ya yabawa uwar Jam’iyyar bisa yadda suka bayyana kawo ziyarar Jake ga gwamnati da al’ummar jihar Yobe kan abin bakin ciki da takaici da ya faru.

Ya ce: “Wannan ziyarar ta sa mun fahimci  cewar lalle uwar Jam’iyyar mu ta nuna matukar damuwar ta kan halin da muke ciki, sakamakon  sun kula da mu.

“A madadin gwamnati da mutanen jihar Yobe, na gode kuma ina godiya da zuwan ku.”

Ya kuma ba da tabbacin hadin kan gwamnatin sa domin inganta hadin gwiwa da hukumomin tsaro.

Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafawa sojoji, ‘yan sanda, sauran kungiyoyin tsaro, da kuma kungiyar ‘yan banga domin karfafa tsaro a fadin jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments