Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamnatin jihar Yobe ta raba tallafin kudi ga iyalan wadanda harin ‘yan tada kayar baya ya rutsa da su a garin Mafa da ke karamar hukumar Tarmuwa a kwanakin baya.
Alhaji Mala Misty, mai baiwa gwamna Mai Mala Buni shawara kan harkokin ilimi mai zurfi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Damaturu.
Gwamnan wanda mataimakinsa Alhaji Idi Barde Gubana ya wakilta, tun baya ya ambata bayar da gudunmawar Naira miliyan 30 domin tallafa wa iyalan wadanda abin ya shafa, baya ga gudunmawar da sauran masu jajantawa suka bayar.
An raba kudaden ne ga iyalai 128 da suka rasa rayukansu da kuma wadanda harin ya raba da muhallansu, domin rage tasirin lamarin.
Daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin da suka hada da Malama A’isha Danbade da Malam Mustapha Muhammad sun mika godiyarsu ga gwamnan da sauran masu jajantawa da goyon bayansu.
Harin da ake kyautata zaton ‘yan ta’addar Boko Haram ne suka kai, ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da raba wasu da dama da muhallin su.