Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiHukumar YSCHMA Ta Gana da Masu Ruwa Da Tsaki, Wadanda Ke Da...

Hukumar YSCHMA Ta Gana da Masu Ruwa Da Tsaki, Wadanda Ke Da Rijista Da Hukumar  A Karamar Hukumar Fika A Yobe

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

A kokarin da ta ke Yi na ganin ta fadada ayyukan ta kan Inganta kiwon lafiya a jihar Yobe Hukumar bayar da gudummawa kan harkokin kiwon lafiya ta Jihar Yobe (YSCHMA) a ranar 3 ga wannan wata na Satumba 2024 karkashin jagorancin babban sakataren hukumar, Dakta Babagana Tijjani ta fara taron ta a karamar hukumar Fika  da masu ruwa da tsaki da masu rajista da hukumar  wadanda suka ci gajiyar shirin a mataki   daban-daban na tsarin bayar da gudunmawar kiwon lafiya na hukumar ta YSCHMA a cikin jihar.

A cikin takardar sanarwar gudanar da wannan taro da ya bayar ga manema labarai babban jami’n hulda da jama’a da harkokin yada labarai na hukumar YSCHMA na Jihar, Malam Sulaiman Gambo Yusuf (Bakoro) ya ambata cewar a  yayin taron, Sakataren zartarwa na hukumar, Dakta Babagana Tijjani ya tabbatar wa wadanda suka ci gajiyar ingantacciyar hidimar kiwon lafiya a fadin jihar.

Dakta Babagana Tijjani ya bayyana cewa taron na daya daga cikin kokarin tabbatar da samar da ingantacciyar hidima kan harkokin na kiwon lafiya  ga wadanda suka yi rajista domin samun nasarar samar da kiwon lafiya a jihar nan zuwa  shekara ta 2030 in Allah ya so.

Babban Sakataren hukumar ya  ce, “Wannan taron da ake gudanarwa a babban  zauren taron wannnan karamar hukuma ta Fika da ya hada da  masu rajista da hukumar da ke cin gajiyar shirin hade da masu ruwa da tsaki ya yi daidai da kokarin da hukumar ke yi na samar da hanyoyin wayar da kan jama’a da kuma cudanya da wadanda suka ci gajiyar tsare-tsaren kiwon lafiya na YSCHMA daban-daban domin fahimtar da jama’a irin rawar da duk masu ruwa da tsaki da abin ya shafa ciki har da YSCHMA, cibiyoyin kiwon lafiya.  , da masu amfana ke takawa.”

Sakataren zartarwar ya sanar da mahalarta taron cewa tare da sabon harajin gudanar aikin hukumar ta  YSCHMA da jerin farashin magunguna, ya kamata masu rajista suyi tsammanin mafi inganci da ingantaccen sabis na kiwon lafiya a cikin cibiyoyin kiwon lafiya na YSCHMA da aka amince da su a duk fadin jihar.

A nasa jawabin, Daraktan tsare-tsare na hukumar, Ahmed Mustapha ya bayyana makasudin gudanar da taron hukumar ta YSCHMA da cewa an yi hakan ne domin kara fahimtar juna a kan tsare-tsaren kiwon lafiya na hukumar YSCHMA, da karbar ra’ayoyin wadanda suka ci gajiyar shirin, da tunatar da wadanda suka yi rajistar hakkokinsu da abubuwan da suke da su da kuma irin rawar da cibiyoyin kiwon lafiya a ƙarƙashin tsarin bayar da gudummawar lafiya na YSCHMA da sauransu ke takawa.

Babban abin da ya fi daukar hankali a taron shi ne gabatar da kwafi da dama na jagora ga masu rajista da masu ruwa da tsaki kan yadda ake gudanar da shirye-shiryen hukumar ta YSCHMA daban-dabam da Daraktan tsare-tsare na hukumar, Ahmed Mustapha ya yi a madadin babban sakataren hukumar.

A cikin sakon fatan alheri na daban-daban, wasu mahalarta taron da suka yi jawabi a taron sun yaba wa gwamnatin jihar karkashin gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni kan kafa hukumar ta YSCHMA da sauran hukumomin da ke karkashin ma’aikatar lafiya ta jihar da ya yi.

Daya daga cikin wadanda suka halarci taron a zauren taron, Idrissa Muhammad Bah ya ce, “Daya daga cikin muhimman abubuwan da suka taba faruwa a jihar a ‘yan kwanakin nan da ba za mu taba mantawa da shi ba, shine kafa wannan hukuma mai albarka ta  kula da lafiya ta jihar wato YSCHMA.

Zuwan wannan hukuma ta YSCHMA a jihar ya maye gurbin kudaden da aka saba kashewa a baya daga aljihun ma’aikatan gwamnati da a yanzu suka shigar da kansu cikin shirin kula da lafiya na YSCHMA da sauran wadanda suka ci gajiyar shirin kiwon lafiya na YSCHMA daban-daban.

Masu ruwa da tsaki a wajen taron sun hada da shugaban karamar hukumar Fika, Hon.  Audu Bukar Gadaka wanda ya samu wakilcin shugaban sashin Mulki (Admin) na karamar hukumar Malam Sani Garba Madugu da daraktan huk

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments