Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka kwashe kwanaki uku ana yi ba tare da jinkiri ba ya tafka ɓarna a ƙauyen Natsinta da ke ƙaramar hukumar Jibia ta jihar Katsina a Najeriya.
Ruwan saman dake sauka kamar da bakin kwarya ya janyo rugujewar gidaje 250, lamarin da ya jefa mazauna gidajen cikin halin ƙunci da rashin tabbas.
Ɗan majalisar dokokin jihar Katsina mai wakiltar ƙaramar hukumar Jibia, Hon. Mustafa Yusuf, wanda ya ziyarci yankin da lamarin ya shafa cikin gaggawa a ranar Asabar 17 ga watan Agusta, 2024.
Ya tabbatar wa mazauna yankin cewa majalisar za ta yi duk mai yiyuwa don ganin gwamnatin jihar ta samar da taimakon gaggawa ga waɗanda suka rasa gidajensu.
Da yake bayyana damuwar sa, Hon. Yusuf ya buƙaci masu ruwa da tsaki, da suka haɗa da jami’an gwamnati, shugabannin siyasa, da ƴan kasuwa, da su bayar da gudunmuwarsu don tallafa wa mutanen da abin ya shafa.
Wani mazaunin ƙauyen Natsinta, Mas’udu Lawal ‘Sarkin Yashi’, ya alaƙanta wannan iftila’in da rashin wadatattun magudanan ruwa masu kyau a yankin.
Ya ƙara da cewa, “datsewar wata babbar magudanar ruwa ta kara ta’azzara tasirin ruwan saman da ya yi ɓarnar, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin mawuyacin hali,” in ji shi.
Kansila mai wakiltar mazaɓar Ƙusa, Shamsu Hassan, ya bayyana ruɗani da aka samu bayan faruwar lamarin.
Inda ya ce, mazaunan da suka rasa matsugunansu na kokawa don samun mafaka domin rage raɗaɗin halin da suke ciki.
Daga cikin waɗanda abin ya shafa, Abdulrahman Ibrahim da Amina sun ba da labarin yadda asarar ta shafe su, inda suka ƙara da cewa ba gidajensu kaɗai suka rasa ba, har ma da muhimman kayyakinsu na amfanin yau da kullum, lamarin da ya ƙara dagula musu halin da suke ciki.
Jaridar Hausa Abcnews ta ruwaito cewa, abin farin ciki, ba a sami rahoton asarar rayuka ba, ko da yake wasu mutane kaɗan sun sami raunuka a lokacin faruwar iftila’in.
Ɗan Madamin Katsina Hakimin Ɗaddara, Alhaji Usman Usman Nagoggo, ya nuna matukar damuwarsa kan yadda jama’a ƙauyen ke cikin wannan hali.
Ya kuma yi kira ga jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su tausayawa al’ummar da abin ya shafa tare da aiwatar da matakan daƙile afkuwar irin haka nan gaba.
A yayin da al’ummar kauyen Natsinta ke kokawa kan wannan iftila’in da ya afku. Ana sa ran ci gaba da ƙoƙarin gyara yankin da abin ya shafa, tare da ƙudirin aniyar shawo kan wannan lamarin.