Wednesday, January 21, 2026
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiGwamna Buni  Ya Bukaci Al'ummar Ngalda Da Su Kula Da Kasuwar Da...

Gwamna Buni  Ya Bukaci Al’ummar Ngalda Da Su Kula Da Kasuwar Da Ake Gina Musu

Daga Sani Gazas Chinade Damaturu

Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya duba kasuwar zamani ta Ngalda da ake ginawa wadda ana gab da kammala gina ta.

Gwamnan wanda ya samu rakiyar mataimakinsa, Hon.Idi Barde Gubana, ya bayyana jin dadinsa da yadda ake gudanar da aikin ba tare da samun wani Jinkirin ko tsaiko ba.

Ya nuna Jin dadin sa dangane da yadda aikin Gina kasuwar ke gudanar musamman yadda Dan kwangilar ke gudanar da aikin akan lokaci don tabbatar da an aiwatar da aikin a cikin wa’adin kammala kwangilar da aka ba shi.

“Ita dai wannan kasuwa ta Ngalda tana daya daga cikin manyan kasuwannin jihar da gwamnatin Jihar ke hobbasan kasuwa irin ta zamani, wadda gwamnati ta gina kasuwar ne domin samar da yanayi mai kyau na harkokin kasuwanci don bunkasa da inganta tattalin arzikin yankin da Jihar Yobe Baki daya.

“Mun gina wasu kasuwanni biyu makamantan wannan kasuwa a garuruwan Yunusari da Machina don tallafawa ci gaban tattalin arziki.”

“Ina kira ga jama’a da aka gina wadannan  kasuwanni, su tabbatar da kula da su yadda ya kamata domin gwamnati ta samu darajar kudinta.”

Tun da farko, kwamishinan gidaje na jihar Ahmed Buba Kyari, wanda ya zagaya da Gwamnan kasuwar ya ce dan kwangilar ya gudanar da aikin ne bisa ka’ida da kayyade lokacin kwangilar da aka ba shi tun farko.

Ya ce aikin wannan kasuwa na gab da kammala kuma nan ba da dadewa ba za a kaddamar da ita yadda harkokin kasuwanci zai Inganta lura da cewar, kasuwar ta Ngalda kasuwace da Masu saye da sayarwa ke zuwa daga ko’ina a fadin Jihar Yobe da ma sauran Jihohin makwbta.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments