Wednesday, January 21, 2026
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeSiyasaGwamna Buni Ya Bayyana Al'umar Yobe Da Ginshikin Dimokaradiyya

Gwamna Buni Ya Bayyana Al’umar Yobe Da Ginshikin Dimokaradiyya

Daga Sani Gazas Chinade Damaturu

Gwamnan jihar Yobe, Hon.  Mai Mala Bun, ya bayyana al’ummar jihar a matsayin ginshikan dimokuradiyya na gaskiya domin tallafawa manufofin gwamnati da shirye-shirye a jihar.

A wata sanarwa da ke dauke da sa hannun Mamman Mohammad daraktan hulda da manema labarai na gwamnan ya ce, gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin bikin zagayowar ranar dimokuradiyya a Najeriya.

Ya ce goyon bayan da jama’a ke ba wa manufofi da tsare-tsare na gwamnati ko shakka babu ya kara karfafa dimokradiyya a jihar.

Gwamnan ya lura cewa shekaru 26 na mulkin dimokuradiyya ba tare da katsewa ba a Najeriya ya baiwa jama’a damar shiga harkokin  gwamnati.

Ya bayyana cewa nade-naden  da gwamnatin sa ta yiwa matasa a matsayin kwamishinoni, shugabannin hukumomin gwamnati, masu ba da shawara na musamman, mataimaka na musamman da masu zaman kansu ya inganta harkokin mulki a jihar.

“Abin farin ciki ne yadda dimokuradiyya ta ba da dama ga jama’a su fadi ra’ayoyinsu da kuma shiga harkokin mulki.

“A jihar Yobe, mun kiyaye manufar bude kofofin mu ga al’umma domin baiwa jama’a damar bayar da gudummuwarsu wajen gudanar da mulki, kuma hakan ya baiwa al’ummar Jihar sanin hakikanin hakkokin su.” Inji shi.

Gwamna Buni ya ce akwai makoma mai albarka ga jihar da kasa tare da sa hannun matasa a harkokin siyasa da gudanar da mulki.

Ya kuma ba da tabbacin karin samun romon dimokuradiyya domin inganta rayuwar al’umma, yana mai cewa, za a kammala dukkan ayyukan da ake gudanarwa domin gwamnati ta samu kimar kudinta, kuma ayyukan su kasance masu amfani ga jama’a.

Gwamnan ya yi kira da a kara ba da hadin kai domin dimokuradiyya ta samu ci gaba da inganta shugabanci na gari.

Buni ya bukaci jama’a da su yi amfani da damina wajen rungumar noma, tallafa wa jami’an tsaro da inganta kyawawan dabi’un zaman lafiya a jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments