Wednesday, January 21, 2026
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiSakon Sallah: Gwamna Buni Ya Bada Tabbacin Taimakawa Harkokin Tsaro, Noma, Samar...

Sakon Sallah: Gwamna Buni Ya Bada Tabbacin Taimakawa Harkokin Tsaro, Noma, Samar Da Ababen More Rayuwa

Daga , Sani Gazas Chinade, Damaturu

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni , ya taya al’ummar musulmi murnar zagayowar bikin Eid-el-kabir, inda ya ba da tabbacin tallafa wa al’umma wajen samar da tsaro, noma da samar da ababen more rayuwa.

A cikin sanarwar da Mamman Mohammad daraktan harkokin ‘yan jaridu da hulda da manema labarai ya fitar ya ce, gwamnan shawarci al’ummar musulmi da su rungumi darussan Idi na sadaukarwa, sadaka da soyayya ga makwabta, ‘yan’uwa da abokan arziki ba tare da la’akari da bambancin siyasa, addini da al’adu ba.

Gwamna Buni ya bayyana bikin Eid Mubarak a matsayin wata dama ga jama’a na gida da kuma mahajjata a Saudiyya don ci gaba da yi wa jihar Yobe da Najeriya addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Gwamnan ya bada tabbacin cewa a cikin shekaru biyu masu zuwa gwamnatin sa za ta kara kaimi wajen inganta tsaro mai dorewa, noma da samar da ababen more rayuwa ga al’ummar Jihar.

Don haka ya bukaci jama’a da su yi amfani da saukar damina domin su tsunduma cikin harkar noma
samar da abinci da wadatar tattalin arziki.

Ya shawarci al’ummomin da ke kusa da rafuka, koguna da wuraren da ake fama da ambaliyar ruwa da su yi taka-tsan-tsan tare tarae da amfani da shawarwarin da hukumomin da abin ya shafa suka bayar game da ambaliyar ruwa a lokacin damina.

Gwamna Buni ya yabawa al’ummar jihar bisa jajircewa da goyon baya da kuma hadin kai ga manufofin gwamnati da tsare-tsare wanda ke karawa gwamnatinsa kwarin guiwa wajen alffahari nasarorin da aka samu a fadin jihar.

“Ina fatan sadaukar da nasarorin da wannan gwamnati ta samu don samun goyon baya da fahimtar ku, tare, za mu ci gaba da inganta rayuwar al’ummarmu,” in ji Gwamna Buni.

Ya yabawa hafsoshi da sojojin Najeriya da sauran jami’an tsaro, ‘yan banga da kungiyoyin mafarauta bisa jajircewarsu wajen ganin an inganta tsaro a jihar.

“Ya kamata mu ci gaba da ba da hadin kai da tallafa wa jami’an tsaro da sahihan bayanai masu inganci don inganta hanyoyin da za a bi wajen yaki da rashin tsaro tare,” in ji shi.

Gwamnan ya yi addu’a tare da yi wa al’ummar jihar da Najeriya fatan samun zaman lafiya da kwanciyar hankali, tare da yin kira ga iyaye da su rika lura da ‘ya’yansu, sannan ya gargadi masu ababen hawa da su guji tukin ganganci a yayin bikin

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments