Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Rundunar ‘yan sandan Jihar Yobe ta bada tabbacin samar da Ingantaccen tsaro a yayin bukuwan sallah.
Tabbacin hakan dai ya fito ne daga bakin kwamishinan ‘yan sandan Jihar CP Emmanuel Ado wanda DCP Saleh Sama’ila ya wakilta a jawabin sa ga manema labarai jim kadan da kammala zaman kwamitin tsaron Jihar wadda sakataren gwamnatin Jihar Alhaji Baban Malam Wali ya jagoranta a madadain gwamnan Jihar Mai Mala.Buni da aka gudanar a babban dakin taro na ofishin sakataren gwamnatin Jihar a Damaturu.
Kwamishinan ya kara da cewar, duk wani shiri don kare rayukan jama’a da dukiyoyin su rundunar da sauran jami’an tsaron da ke jihar sun yi shi akai illa fatan su shi ne Allah SWT ya sa a kammala lafiya.
Rundunar ta kuma raba jami’an ta kowane lungu na Jihar tare da ba su umarnin sa ido da daukar matakin ba sani ba sabo ga duk wata barazana da ke iya kunno kai dangane da harkokin tsaron don magance ta cikin lokaci.
Don haka sun roki jama’a da su gudanar da harkokin sallah cikin nutsuwa ba tare da wani tashin tashina ba domin rundunar ba za ta ta ba yin kasa a gwiwa ba don yin maganin duk wani ko wasu da ke iya haddada fitina cikin jama’a ba musamman a wannan lokaci na sallah.
Wannan taro akan tsaro dai ya samu halarta babban mai bada shawara kan harkokin tsaro ga gwamnan Mai Mala Buni Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam (RTD) tare da sauran manya-manyan jami’an hukumomin tsaron da ke Jihar.


