Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamnatin Jihar Yobe ta shirya tsaf don gudanar da taronta na farko da Gwamna Mai Mala Buni zai amsa tambayoyin al’ummar Jihar kan yadda ya ke gudanar da gwamnatin sa domin cika shekaru shida a kan karagar mulki da kuma nuna nasarorin da gwamnatinsa ta cimma.
Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin Dokta Ibrahim Yabani, mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai a yayin ganawa da manema labarai a ranar Asabar, inda ya bayyana hakan a matsayin wata babbar dama ga ‘yan jihar da ‘yan jarida da masu ruwa da tsaki na yin hulda kai tsaye da gwamnan ba tare da samun wani tsaiko ba.
Ya kara da cewa, taron zai samar da gaskiya da rikon amana ta hanyar ba da damar tattaunawa kan batutuwan da suka shafi al’umma.
Dokta Yabani ya bayyana cewa taron zai baiwa jami’ai damar raba sabbin tsare-tsare da kuma tattara ra’ayoyin jama’a, biyo bayan wani irin ya haka da ake amfani da shi cikin nasara a wurare kamar Amurka.
A wannan taro da za’a gudanar Gwamnan a shirye yake ya amsa tambayoyi gaba da gaba daga dukkan mahalarta taron ba ‘yan jarida kadai ba.
Ya kara da cewa “‘yan jihar za su iya yin tambaya game da alkawuran da aka yi, da ci gaban da aka samu, da kuma kalubalen da aka fuskanta.”
Dokta Yabani ya jaddada rawar da irin wannan taron ke takawa wajen inganta ka’idar ‘yancin labarai tare da tabbatar da tattaunawa mai inganci.
Taron wanda zai gudana a ranar 29 ga watan Mayu, 2025, na da nufin karfafa amincewa tsakanin gwamnati da jama’a, tare da fatan sanya shi ya zama ruwan dare a harkokin mulkin.


