Daga Sani Gazas hinade, Damaturu
Sabon Shugaban Jam’iyyar PDP Sanata (Amb) Umar El-Gash, wanda ya sake zama shugaban jam’iyyar a jihar Yobe a zaben da aka gudanar a ranar asabar, ya yi alkawarin sake farfado da jam’iyyar tare da mayar da ita wata fitilar fatan alheri ga al’ummar jihar Yobe.
Sabon Shugaban ya bayyana hakan ne a jawabin sa na nuna godiya da kuma nuna matukar jin dadinsa, tare da amincewa da amana da amincewar da ‘yan jam’iyyar suka yi masa wadda aka gudanar a babban dakin taro na 27 Augusta da ke garin Damaturu fadar Jihar Yobe.
Sanata El-Gash ya jaddada cewa sake zabensa ba wai nasara ce kawai ta kanshi ba, a’a, tare da tabbatar da aniyar jam’iyyar ta tabbatar da dimokuradiyya, da adalci, da kuma gudanar da mulkin kasa baki daya.
Ya yi nuni da cewa nasarar da jam’iyyar su ta PDP ta samu a zaben shugaban kasa na 2023 shaida ce ta jajircewa, aminci, da karfin imanin ‘ya’yan jam’iyyar.
Shugaban jam’iyyar PDP ya yi alkawarin yin aiki tukuru don sake gina jam’iyyar tare da sake dawo da martabar jam’iyyar, tare da tabbatar da cewa ta kasance ta yi fintinkau ta kowane bangaren matakin zabe a sauran jam’iyyun jihar.
“Wasu magoya bayan Jam’iyyar ta PDP. Jihar ta Yobe na ganin sake zaben Sanata El-Gash ya karawa masu kishin jam’iyyar kwarin guiwa, wadanda ke zawarcin ganin jam’iyyar ta dawo da martabarta a da a jihar ta Yobe baki daya.”
“A cewar ma su wadannan furuci kamar Ibrahim Bade daga Gashuwa na ganin, yayin da zaben 2027 ke gabatowa, shugabancin El-Gash zai taka muhimmiyar rawa wajen tsara samun nasarar jam’iyyar a kowane bangaren lura da irin nasarar da Jam’iyyar ta samu a zaben da ya gabata na 2023 yadda ta kai ga lashe kujerun majalisar tarayya ta kasa guda biyu da na Jihar guda biyu wadda hakan ‘yar muniniya ce na samun nasarar Jam’iyyar a zaben 2027 in Allah ya mai mu..in ji Ibrahim Bade.”
Jam’iyyar PDP a jihar Yobe za ta bukaci yin aiki da dabaru don kiyaye dacewarta da kuma kira ga masu kada kuri’a.


