Thursday, May 15, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiGwamna Buni Ya Bukaci NDLEA Ta Kawo Karshen Ta'ammali Da Miyagun Kwayoyi...

Gwamna Buni Ya Bukaci NDLEA Ta Kawo Karshen Ta’ammali Da Miyagun Kwayoyi A Jihar Yobe

Daga Sani Gazas Chinade Damaturu

Gwamnan Jihar Yobe,  Mai Mala Buni ya yi kira ga kwamandan hukumar hana sha da fataucin muggan kwayoyi ma su sa maye (NDLEA) mai kula da shiyya ta 1 da ta kunshi jihohin Bauchi, Yobe da Borno, ACGN Marcus Ayuba da ya tashi haikan don yin yaki domin dakile yaduwar muggan kwayoyi sa maye da ta’ammali da su da ake yi musamman a tsakanin matasa a fadin jihar ta Yobe.

Gwamnan ya yi kiran ne a lokacin da kwamandan shiyyar ya kai masa ziyarar ban girma a gidan gwamnati da ke Damaturu.

Ya jaddada bukatar kara hada kai da hadin gwiwa da hukumar domin yaki da sayar da miyagun kwayoyi a jihar.

Ya kuma kara da cewa shaye-shayen miyagun kwayoyi na da alaka kai tsaye da aikata laifuka, don haka ya bukaci kwamandan shiyyar da ya kara himma tare da hada kai da hukumomin da abin ya shafa wajen yakar shan miyagun kwayoyi da masu safarar su.

Buni ya yi kira ga kwamandan Hukumar ta NDLEA da ya kawo karshen shaye-shaye a Jihar Yobe.

Gwamnan ya samu wakilcin mataimakinsa Hon Idi Barde Gubana wanda ya bada tabbacin gwamnati za ta cigaba da bada goyon baya da kuma shirye shiryen kawar da wannan illa da shaye-shaye ke haifarwa a jihar.

Tun da farko a jawabinsa  kwamandan shiyyar ACGN Marcus Ayuba ya sanar da gwamnan cewa ya je jihar ne a ziyarar wayar da kai da nufin inganta ayyukan ma’aikatan sa.

Ya yaba da hadin kai da goyon bayan da ake baiwa rundunar jihar, ya jaddada cewa gwamnatin jiha ce babbar mai ruwa da tsaki a yaki da shan miyagun kwayoyi.

Ya kuma jaddada aniyar jami’an sa na tabbatar da bin ka’idojin yaki da safarar miyagun kwayoyi na kasa da kasa da kuma yaki da fataucin miyagun kwayoyi a shiyyar da ma Nijeriya baki daya.

A madadin shugaban zartaswa na hukumar kula da sha da fataucin muggan kwayoyin sa maye  na kasa, na gabatar da wasiƙar godiya ga gwamnatin jihar saboda damuwarta da goyon bayan da ta ke nunawa ga rundunar da ke  jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments