Monday, May 12, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiKungiyar Matasan Afenifere Ta Bukaci Tinubu Ya Sauke Hafsoshin Tsaro Na Kasa...

Kungiyar Matasan Afenifere Ta Bukaci Tinubu Ya Sauke Hafsoshin Tsaro Na Kasa Akan Gazawarsu

Daga Abdullahi Inuwa

Kungiyar matasan Afenifere Youth Vanguard for Peace in Nigeria (AYPN) ta yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya sauke duk wani jami’in tsaro da ya kasa sauke nauyin da ya rataya a wuyansa, musamman sakamakon gazawar da ake ci gaba da fuskanta a fannin tsaro a faɗin ƙasar.

Wannan kiran ya biyo bayan maganar da dan majalisar wakilai daga Plateau, Hon. Yusuf Gagdi, ya yi yayin zaman majalisa, inda ya nuna damuwarsa kan yadda ‘yan ta’adda ke kara samun karfi, yana mai bayyana yadda masu tayar da kayar baya suka kwace sansanonin sojoji da manyan motoci na yaki har 40 a Jihar Borno.

Gagdi ya bayyana cewa wannan lamari babban barazana ne ga zaman lafiya da tsaron kasa, yana mai tambaya ko Najeriya na da cikakken iko da kariyar iyakokinta.

A martani ga wannan furuci, shugaban kungiyar AYPN, Olatunji Fadare, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ya caccaki yadda ake tafiyar da ma’aikatar tsaro, yana mai kira ga Shugaban Ƙasa da ya gaggauta daukar matakin sauya shugabancin ma’aikatar.

“Babu wata hujja da za a bayar kan yadda ake gudanar da harkokin tsaro a halin yanzu. Wannan ba wajen raba kwangila ba ne ko lada ga ‘yan siyasa; ma’aikatar tsaro ce ginshikin kariyar kasar nan,” in ji Fadare.

Kungiyar ta AYPN ta zargi ma’aikatar tsaro da yin kunnen uwar shegu ga gargadin gwamnoni da ‘yan majalisa. Ta ce ma’aikatar ta yi biris da gargadin da Gwamnan Jihar Borno ya yi game da barazanar tsaro a yankinsa, kamar yadda Hon. Gagdi ya bayyana.

“Idan gwamnoni da ‘yan majalisa da ke tsaka da kare rayukan al’umma sun yi kira, amma a mayar musu da karyar zargi, hakan yana nuna gazawar da ke cikin shugabancin ma’aikatar. Rainin hankalin masu kishin kasa na kara bai wa ‘yan ta’adda damar cin karensu ba babbaka,” a cewar Fadare.

AYPN ta bukaci a sake fasalin tsarin tsaron kasar ta hanyar zabar masu cancanta ba tare da la’akari da biyayya ga jam’iyya ko siyasa ba.

Ta kara da cewa idan aka ci gaba da nuna halin ko in kula da kashe-kashe da sace-sace da kuma gazawar rundunonin soja, hakan zai rage wa jama’a kwarin gwiwa ga gwamnatin tarayya.

“Jinin sojojinmu da na al’ummar da aka rasa yana bukatar adalci. Kuma adalci zai samo asali ne daga sauke wadanda suka gaza kare lafiyar ‘yan kasa,” in ji Fadare.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments