Monday, May 12, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiGagdi Yaja Hankalin Gwamnati Da Ta Guji Fushin Yan Kasa Akan Rashin...

Gagdi Yaja Hankalin Gwamnati Da Ta Guji Fushin Yan Kasa Akan Rashin Tsaro

Daga Abdullahi Inuwa

Ɗan majalisar wakilai daga Jihar Filato, Honourable Yusuf Adamu Gagdi, ya bayyana fargaba kan tabarbarewar tsaro a Najeriya, inda ya ce rashin ɗaukar mataki daga hukumomin gwamnati na iya jefa ƙasar cikin wani halin rikici da ka iya janyo ƙin jinin shugabanni daga al’umma.

Gagdi ya bayyana haka ne yayin wata muhawara a zauren majalisar wakilai, inda ya ce hotunan da ya gani na harin Boko Haram a barikin Giwa da ke Maiduguri, Jihar Borno, sun tayar masa da hankali matuƙa.

“Za ku gane girman wannan batu ne idan kuka ga hotunan yadda Boko Haram suka ragargaza barikin Giwa. Na firgita, na damu matuƙa kan ko har yanzu gwamnati na iya kare rayukan ƴan Najeriya a cikin ƙasarsu,” in ji shi.

Ya ce an ware kuɗaɗe masu yawa don siyan makamai da manyan motoci na yaƙi, amma duk da haka, Boko Haram na kwace su cikin sauƙi.

“Muna ware kuɗi a kasafin kuɗi don siyan makamai, tankoki da sauran kayan yaƙi, amma a ƙarshe suna shiga hannun maƙiyan ƙasa. Wannan abu ne da ba za a yarda da shi ba,” in ji Gagdi.

Ya yi kira da a hukunta manyan hafsoshin tsaro da sauran shugabannin hukumomin tsaro da suka yi sakaci da nauyin da ke wuyansu.

“Ko da yake muna godiya da ƙoƙarin da jami’an tsaro ke yi na kare rayuka, dole ne a ladabtar da duk wanda ya nuna sakaci. Mun isa nan wajen magana, yanzu lokaci ne na aiki da ɗaukar matakai a hukumance,” in ji shi.

Gagdi ya soki yadda gwamnati ke raina gwamnonin jihohi da ke bayyana matsalolin tsaro a jihohinsu, yana mai cewa yakamata a girmama su a matsayin kwamandan tsaro na jihohinsu.

“Abin takaici ne a ce wani jami’in gwamnati da ke zaune a Abuja zai ce gwamna na tayar da jijiyoyin wuya, alhali mutane na mutuwa a jiharsa,” in ji shi.

Ya kara da cewa idan har gwamnati ba ta dauki mataki cikin gaggawa ba, akwai yiwuwar ƴan Najeriya su ɗauki doka a hannunsu.

“Idan ba mu farka ba yanzu, lokaci na iya zuwa da jama’a za su daina bambanta mu da ƴan ta’adda ko barayin gwamnati. Za su fara fuskantar mu kamar yadda suke fuskantar maƙiyansu,” in ji shi.

Gagdi ya yi alkawarin mikawa majalisar bayanan sirri da hotuna da ke nuna yadda makaman da aka siya don yaƙi da ta’addanci ke faɗa hannun Boko Haram.

Ya kammala da kira ga ƴan majalisa da su dage wajen ganin gwamnati na aiki da kashedin da majalisar ke bayarwa, ba kawai ta hanyar fitar da sanarwa ba, illa dai a aikata hakan a kasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments