Daga Sani Gazas Chinade Damaturu
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da sayo motocin sintiri 5 da babura 30 domin inganta ayyukan sojoji da matasa masu aikin sa kai a garin Izge da ke karamar hukumar Gwoza a Jihar Borno.
Motocin sintiri da babura suna da nufin inganta harkokin tsaro ne ga matasa ‘yan sa kai, kan tsaro na cikin gida, da ba su damar mayar da martani cikin gaggawa ga barazanar da kuma tallafawa ayyukan soji a cikin al’ummarsu.
Zulum ya amince da hakan ne a ranar Jumu’a yayin ziyarar tantancewar irin barnar da ‘yan ta’adda suka yi da ya kai Gwoza.
Gwamnan ya yabawa sojojin Najeriya da al’ummar yankin bisa jajircewar da suka yi wajen dakile hare-haren ‘yan tada kayar baya. “Na zo nan ne don in bincika halin da ake ciki a kasa kuma in gano daga gare ku menene ainihin matsalolinku don mu magance su,” in ji shi.
“Muna da kwarin gwiwar cewa insha Allahu ba za mu sake yin rashin nasara ba, ina so in yaba wa sojoji duk da wasu kalaman da wasu mutane suka yi ciki har da ni, da muka ce, mun fara ganin sake bullowar Boko Haram, hakan ba yana nufin muna raina aikin sojojin Najeriya ba ne, muna bayyana gaskiyar lamarin ne domin mu hada kai mu magance matsalar da ke kunno kai, domin kada mu yi kasa a gwiwa.”
“Za mu yi duk mai yiwuwa insha Allahu don tabbatar da cewa Izge ba ta rasa matsugunai ba.
Don haka ina so in yaba wa mutanen Izge, dangane da yadda suke da jajircewa matuka.
Za mu yi duk abin da ya kamata don tabbatar da doka da oda a Izge, don haka ku gaya mana abin da ya kamata a yi, kuma za mu yi in Allah ya so.”
A cewar Gwamnan, kayayyakin sun hada da Toyota Hilux guda 5 da kuma babura 30, da sauran kayan aiki.
Zulum ya kuma bayyana shirye-shiryen sake tsugunar da al’ummomin da suka rasa matsugunansu a hankali.
Don haka yana mai tabbatar wa mazauna garin ci gaba da goyon bayan gwamnati don dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin da ma Jihar Borno gaba daya.
Gwamnan ya lura cewa za a sake tsugunar da al’ummomi da dama da suka hada da Ashigasha, Warabe, Guduf, Wala, da sauran kananan kauyuka da dama.
Zulum ya samu rakiyar dan majalisa mai wakiltar Gwoza a majalisar dokokin jihar, Abdullahi Buba Abatcha, shugaban ma’aikata, Dr Muhammad Ghuluze, kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, Sugun Mai Mele, babban sakatare a gidan gwamnati, Mustapha Ali Busuguma, babban mai bawa gwamna shawara, Dr Mairo Mandara, da sauran jami’an gwamnati.