Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamnan jihar Yobe Hon. Mai Mala Buni a ranar alhamis ya ziyarci Hedikwatar Task Force Brigade ta 27 Buni Gari, domin jajantawa wadanda aka kashe kan harin da ‘yan tada kayar baya suka kai.
A cikin jawabinsa Gwamna Buni ya bayyana abin takaici ne ga sake barkewar tashe tashen hankula da kuma hare-haren da ake kaiwa jami’an tsaro.
Gwamnan ya jajanta wa sojoji da iyalan ma’aikatan da suka mutu, yana mai cewa, “Jami’an ba su mutu a banza ba, sun mutu suna kokarin kare kasarsu sosai”.
Ya bayar da tallafin N2m ga kowane iyalan jaruman da suka mutu, sannan kuma N1m ga jami’an da suka samu raunuka.
Buni ya ce gwamnati za ta kuma bayar da tallafin ilimi kyauta ga yaran sojojin da suka mutu.
Hakazalika, Gwamnan ya sanar da bayar da gudunmuwar Naira miliyan 50 da za a raba wa dakarun rundunar ta 27 Brigade Buni Gari, baya ga kayan abinci, katifa, barguna, da sauran kayayyaki da gwamnatin jihar ta bayar.
Ya kuma ba da tabbacin goyon bayan gwamnati da al’ummar jihar ga sojoji da sauran jami’an tsaro domin yakar wadannan ‘yan ta’addan yadda ya kamata tare da fatattakarsu.
Gwamna Buni ya ba da umarnin karfafa tsaro a kewayen rundunar, inda ya ba da tabbacin goyon bayan gwamnati ga jami’an tsaro “Za mu ci gaba da kara kaimi wajen inganta tsaro a kewayen ku”.
Kwamandan rundunar Birgediya Janar Usman Ahmed, wanda ya jagoranci Gwamnan wajen duba wannan runduna, ya yabawa Gwamna Buni kan yadda ya ke nuna damuwa da kulawa ga sojojin a kowane lokaci