Thursday, May 15, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiMakiyan Matawalle Sun Ji Kunya - Suleiman Shu'aibu Shinkafi

Makiyan Matawalle Sun Ji Kunya – Suleiman Shu’aibu Shinkafi

An bayyana ministan kasa a ma’aikatar taaron tarayyar Najeriya Dokta Bello Muhammad Matawalle a mataayin mutum jajirtacce mai yin ayyukan kokarin ceto kasa tare da jama’arta baki daya domin a ci gaba da samun ci gaba duk da ya na da makiya.

Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da wakilinmu

“Babbam dalilin da ya sa nake gayamaka haka shi ne Matawalle na tare da Allah”.

“Muna sane Matawalle na da makiya da yawa, amma shi Matawalle a koda yaushe duk abubuwan da yake na ci gaban kasar nan ne da kuma ci gaban arewacin kasar nan a kida yaushe”.

Suleiman Shinkafi ya ci gaba da cewa “ai su tuni sun saba da jin haka irin wadannan rubuce – rubucen da wasu ke yi, idan ma baka da makiya to sai kaje ka nema, don haka daga gani makiya ne ke yada irin wannan labarai na karya don biyan wata bukatar son zuciya kawai”.

Saboda haka muke yin kira ga jami’an taaro da su yi gaggawar kama irin wadannan mutane masu yada bayanan kanzon kurege don kawai su yi batanci ga wani kuma irin hakan ana karkatar da hankulan mutane ne kawai kuma hakan ba siyasa ba ce, me ya sa wasu mutane wasu  ba su son mai taimakon kuma wasu mutane ba su son wanda Allah ya daukaka, ko mutum yaso ko ya ki Allah ya daukaka Matawalle kuma Allah ya dataja Matawalle a cikin mutane miliyan dari biyu da Tamanin ya ba shi ministan tsaro ya na kuma kula da harkokin tsaron, sai makiyin Allah ne kaaai zai ce bai yi wani abu ba domin duk inda ake da matsala zai je ya bincika ya kuma kai Sojoji wurin ayi abin da ya dace”.

“Kuma ga yan Najeriya na kwarai wadanda ba makiya Allah ba kuma ba yan bakin ciki ba  sun san Matawalle babu irinsa, ina tabbatar maku da cewa ba a taba samun mutum ministan taaro kamar yadda Matawalle yake yi ba domin ya tashi tsaye ya Sadaukar da kansa wajen ganin an samu cikakkrn tsaron lafiya da dukiyar jama’ar kasa baki daya, don haka mutanen kirki masu kauna da son Najeriya Sun sani cewa ya na iyakar bakin yin sa”.

Saboda haka ina kara bashi shawarar cewa ya ci gaba da aikinsa da duk kokarin bayar da irin nasa gudunmawar wajen ci gaban kasa da al’ummarta domin hassada ga mai rabo Taki ce dole ne su ganshi su kuma batshi a inda yake ba yadda zaku yi da shi, Matawalle ikon Allah ne ba yadda zaku yi da shi domin Allah ya na bayansa don haka nan gani nan bari kawai ba mai iya ja dashi duk kuma wanda ya ja da shi gwiwarsa za ta yi kasa saboda ba mai iya ja da ikon Allah, don haka muna tare da mai girm matawalle saboda haka ne muke yin kira ga al’ummar Najeriya cewa su ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga Matawalle da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ke kokarin kawo tsare – tsaren ci gaban kasa wanda ake gani kuma muna tabbatarwa da jama’a kowa zai gani cikin ikon Allah da dimbin isuwarsa.

“Ina ba yan Najeriya tabbacin cewa in dai akwai irin su Matawalle kasar nan za ta saitu har al’amura su kara inganta, don haka tsaro fa aiki ne na sai kowa ya bayar da gudunmawarsa a kasa kuma ya dace jama’a su sani cewa batun matsalar tsaro lamari ne da ya shafi dukkan duniya kuma a Najeriya hukumomi na iyakar bakin kokarin magance shi don haka muna ganin abubuwan da suke faruwa za kuma mu ci gaba da yi masu addu’a ta alkairi in Allah ya yarda, ina godiya ga yan Najeriya masu fahimta”.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments