Saturday, April 26, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabarai‘Yan Sanda Sun Bankado Wani Rumbun Makamai A Akwa Ibom

‘Yan Sanda Sun Bankado Wani Rumbun Makamai A Akwa Ibom

Daga Abdullahi Inuwa

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Akwa Ibom ta samu nasarar bankado wani babbar ma ajiyar makamai da harsasai na ‘yan ta’adda, a wani samame da suka kai da safiyar yau a garin Ikot Ekpene.

A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, DSP Timfon John, ya fitar, ya bayyana cewa an gudanar da samamen ne da misalin ƙarfe 5:15 na safe, inda aka cafke wani mutum mai suna Monday Maurice Okoko, mai shekaru 72 da haihuwa, da ake zargi da sarrafa wannan ajiyar makamai ba bisa ƙa’ida ba.

Bincike a gidansa yasa an gano wata babbar taska ta makamai da suka haɗa da Bindiga mai salon ribalba da aka ƙera a gida, Bindiga ƙarama da ake rage ma tsawo, ƙirar gida, Bindiga mai dogon bututu ƙerir gida da kuma Bindiga nau’in LAR da aka ƙera a gida kana wasu Bindigu biyar nau’in Dane, tare da  Gubar harsasai da kuma alburusai nau’in Borries.

Hukumomi sun bayyana cewa ana zargin makaman da aka gano suna hannun ƙungiyoyin ‘yan ta’adda da ke addabar wasu sassan jihar.

DSP John ya ƙara da cewa bincike na farko yana ci gaba, kuma ana kokarin kamo sauran mambobin ƙungiyar da ke da alaƙa da wannan lamari.

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Akwa Ibom ta sake jaddada kudurinta na yaki da miyagun laifuka da tabbatar da tsaron lafiyar al’ummar jihar.

 

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments