Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Kungiyar makiyaya ta Kulen Allah ta Najeriya, KACRAN, ta yabawa ministan ma’aikatar kula da dabbobi, Alhaji Idi Maiha bisa jajircewarsa na bunkasa fannin.
Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar na kasa Hon. Khalil Moh’d Bello yayin tattaunawar sa da wakilinmu yadda ya kara da bayyana irin gagarumar gudunmawar da aka bayar a wajen taron bitar na kwanaki biyu da ma’aikatar kula da kiwon dabbobi ta shirya tare da hadin gwiwar shirin SPRING na Burtaniya.
A cewar sa, wannan taron bitar ya samar da dandalin tattaunawa kan hanyoyin da dabarun zamani da nufin inganta kiwon dabbobi da kuma samar da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya.
“A matsayinmu na daya daga cikin kungiyoyin makiyaya da suka halarci wannan gagarumin bita, mun samu kwarin guiwa ne da irin jawaban da minista, Alhaji Idi Maiha ya gabatar.”
A cewar sa jawabin nasa ya gamsar da kusan duk wadanda suka halarci taron, wadanda suka hada da su kan su ma’aikatan ma’aikatar, wakilai daga aikin SPRING na Burtaniya, ‘yan jaridu, da mu shugabannin kungiyoyin makiyaya da sauran masu ruwa da tsaki, inda suka tabbatar da cancantarsa bIsa ga irin shirye-shiryen jagorancin da a wannan sabuwar maa’aikata ta kula da dabbobi.
“Ministan ya taka rawar gani a duk tsawon wannan bitar, inda yake amsa tambayoyi daga mahalarta taron wanda ya nuna himmarsa ta yin tattaunawa ta hadin gwiwa, a matsayinsa na gogaggen manomin kiwo, wanda ke da masaniya kan ayyukan kiwo ba kawai a Najeriya ba, har ma a yammacin Afirka wadda ya sake farfado da fata da kwarin gwiwa na makiyaya da masu ruwa da tsaki.”
“Kafin kafa ma’aikatar kiwon dabbobi da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa, kyakkyawan fata da ke tattare da makomar kiwo a Najeriya ya yi kasa sosai.
“Wani muhimmin abin da ke cikin jawabin ministan, wanda ya dace da manufofinmu, shi ne yadda ya mayar da hankali sosai wajen samar da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin makiyaya da manoma, ya jaddada cewa ba za a iya samun ci gaba ba sai da tushen zaman lafiya.
Hoton Shugaban kungiyar Kulen Allah na kasa Honarabul Khalid Muhammad Bello