Sunday, April 27, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiMataimakin Gwamna Jatau Ya Sheke Ministan Harkokin Waje Tuggar Da Mari A...

Mataimakin Gwamna Jatau Ya Sheke Ministan Harkokin Waje Tuggar Da Mari A Fadar Sarki

An samu wani lamari mai cike da drama a Fadar Emir na Bauchi ranar Juma’a, inda aka rawaito cewa Mataimakin Gwamnan jihar, Auwal Jatau, ya mare Ministan Harkokin Waje, Yusuf Maitama Tuggar, a gaban manyan baki ciki har da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima.

Lamarin ya faru ne yayin bikin naɗa tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar, a matsayin Makama Babba 1 na Masarautar Bauchi, wanda ya haɗu da ɗaurin auren diyarsa, Khadija Mohammed.

Majiyoyi sun ce rikicin ya samo asali ne bayan da Ministan ya furta wasu kalamai da ake ganin sun zagi gwamnatin Bala Mohammed — kalaman da Jatau ya ɗauka da zafi matuƙa.

“Mataimakin Gwamnan ya nuna fushi ƙwarai. Abin ya ba da mamaki. Da ba don saurin shigowa da sasanta da Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima ba, da abin ya iya rikidewa zuwa wani abu mafi muni,” in ji wani ganau ga wakilinmu.

Wannan rikici ya sake kunna wutar jita-jitar husuma mai tsanani tsakanin Minista Tuggar da Gwamna Bala Mohammed. Tuggar dai na daga cikin masu sukar gwamnatin PDP mai mulkin jihar Bauchi.

Zuƙaƙƙen masharhanta na siyasa na ci gaba da tofa albarkacin baki, yayin da ba a samu wata sanarwa daga ɓangarorin biyu ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments