Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeSiyasaBa bukatar 'yan jihar Katsina ne a gaban Yakubu Lado Danmarke ba, ...

Ba bukatar ‘yan jihar Katsina ne a gaban Yakubu Lado Danmarke ba,  -Mustapha Inuwa

Ba bukatar ‘yan jihar Katsina ne a gaban Yakubu Lado Danmarke ba,  -Mustapha Inuwa

Shugaban yakin neman zaben dankarar gwamnan jihar katsina a karkashin jam’iyya PDP a shekarar 2023, Dr. Mustapha Inuwa ya bayyana wanda ya yi wa yakin neman zaben zama gwamnan jihar katsina a lokacin, Sanata Yakubu Lado Danmarke a matsayin wanda ba al’ummar jihar katsina ne a gabansa ba, kasuwancinsa ne kawai ya sa a gaba.

Dr. Mustapha Inuwa ya fadi haka ne a cikin wata zantawa da jaridar KatsinaTimes ta yi da shi, bidiyon zantawar da ya bayyana a shafukan jaridar a ranar Alhamis din nan.

Dr. Mustapha ya ce “na yi da-na-sanin yi wa Yakubu Lado shugaban yakin neman Zabe.”

A cewar Mustapha Inuwa, domin ba al’ummar jihar Katsina ba ne a gabansa Yakubu Ladon ba, kawai kasuwancinsa ne ya sa a gaba ba bukatar al’ummar jihar na ya zo ya cece su ba.

“Irin abubuwan da ke faruwa (a tafiyar Yakubu Lado) sai mutum ya yi nadamar a ce yana da hannu cikin abin da ya faru (in ya dafa masa)” In ji shi

“(Ya ta6a fada min cewar) abin da yake tunani ma, irinmu da muke da ‘experience’ mu zo, yana gwamna in yi masa mataimaki. Na yi dariya har na kusa fadowa a gado, don ban taba jin maganar da ta raina min wayau ba irin wannan.” In ji Mustapha

Daga nan ne sai Dr. Mustapha ya kawo wata magana da Ladon ya fada masa cewar zai ba shi wani bangare na kula da kudade a matsayinsa na mataimakinsa bayan sun lashe zabe.

“Sai (Yakubu Lado) ya ce; ai da ma matsalar dai ai na sani tsakanin gwamna da mataimaki ai magana ce ta kudi; Ni in rike ‘federal allocation’, Kai na bar maka na ‘local government’. Wallahi Tallahi abin da ya ce ke nan” In ji Dr. Mustapha.

A saboda da haka, Mustapha ya bayyana nadamarsa karara kan dafawar da ya yi wa Lado a baya, ya kuma ce ya yi da-na-sanin haka, inda ya ce daga lokacin ne ya kuma zare hannuwansa daga lamurransa.

“Maganar gaskiya nadamar da nake yi, da na shiga a cikin hidimarsa a matsayin dantakarar gwamnan, kuma na san cewar wallahi bai cancanta ba.” Ya nanata.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments