Gwamnonin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) a ƙarƙashin PDP Governors Forum (PDPGF) sun bayyana damuwa kan tabarbarewar tsaro a Najeriya, musamman a wasu sassan ƙasar kamar Borno, Filato, Katsina da Edo.
Don haka, forum ɗin ta bukaci sake duba manufofi da dabaru na tsaro, tare da aiwatar da tsarin daga ƙananan matakai (bottom-up approach) wanda zai bai wa jihohi damar ƙarfafa tsaro a yankunansu.
Gwamnonin sun yi Allah wadai da hare-haren baya-bayan nan a jihar Filato, tare da jajanta wa gwamnatin jihar da al’ummarta, musamman waɗanda suka rasa rayuka da dukiyoyi a wannan mummunan lamari.
Har ila yau, gwamnonin sun sake bayyana goyon bayansu ga Mai Girma Gwamnan Jihar Ribas, Sir Siminalayi Fubara, dangane da matsalolin siyasa da jihar ke fuskanta sakamakon ayyana dokar ta-baci. Sun sha alwashin tsaya masa har sai an samu mafita.
Gwamnonin PDP sun bayyana aniyarsu ta dakile duk wani yunkuri na karya tsarin dimokuraɗiyyar kundin tsarin mulki ta hanyar ɗaukar matakin shari’a a kotun ƙoli domin fassara doka game da ayyana dokar ta-baci a kowace jiha.
Dangane da jita-jitar haɗewar jam’iyyun siyasa da ƙungiyoyi, forum ɗin ta ce PDP ba za ta shiga kowace haɗaka ba a fagen siyasar Najeriya. Sai dai PDP a matsayinta na babbar jam’iyyar adawa, za ta karɓi kowane mutum, jam’iyya ko ƙungiya da ke son haɗin gwiwa domin karɓar mulki da samar da shugabanci nagari a shekarar 2027.
Sanarwar taron, wacce Gwamnan Bauchi kuma Shugaban forum ɗin, Sanata Bala Mohammed ya sa wa hannu, ta bayyana cewa PDP za ta yi aiki tare da Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC) da sauran ƙungiyoyi don gudanar da taron NEC a ranar 27 ga Mayu, 2025, da kafa kwamitin rabon mukaman jam’iyya (zoning committee), da kuma gudanar da babban taron jam’iyyar a ranakun 28, 29 da