Daga Sani Saleh Chinade, Damaturu
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni (CON, COMN), a yau ya mika kudin makaranta da kwamfutocin tafi da gidanka ga daliban jihar da suka samu gurbin karatu a makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya.
A wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Gwamna Buni, Mamman Mohammed, ya fitar, ya bayyana cewa dalibai 127 ne suka nemi tallafin karatu kuma kowannensu an ba shi Naira 475,000 da kwamfutar tafi da gidanka domin saukaka karatunsu.
“Ina farin cikin sanar da cewa gwamnatina ta kasance mai daurewa wajen tallafawa dalibai domin ci gaba da karatu a gida da kuma kasashen waje, inda fiye da dalibai 38,000 suka amfana da tsarin tallafin karatu na gwamnati a wannan mulki.”
“Wannan shi ne karo na hudu a jere da gwamnatin nan ke bayar da tallafin karatu ga wadanda suka kammala karatun lauya domin zuwa makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya.”
Gwamna Buni ya kara da cewa daga cikin dalibai 189 da suka karanci fannin lafiya da wasu fannonin dangoginsu a jami’o’in kasar India, 140 daga cikinsu an dauke su aiki, yayin da saura 49 za a daukesu nan bada jimawa ba.
Ya sake jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa ilimi muhimmanci tare da tallafa wa kowane dan jihar wajen samun ilimi a matakai daban-daban.
“Haka zalika, wannan gwamnati za ta ci gaba da tallafawa daliban da ke neman takardun kwarewa a makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya domin su samu damar zama lauyoyi. Haka nan ga masu fannin lissafi a ANAN da ICAN, da kuma masu gudanar da harkokin mulki a ASCON,” in ji shi.
Gwamna Buni ya gargadi daliban da su kiyaye dokoki da ka’idojin makarantar.
“Ya kamata ku kiyaye dokokin da doka ta shimfida a makarantar, ku guji duk wani abu da zai jefa karatunku cikin hadari.”
“Ku kasance jakadu nagari ga jiharmu, domin mu yi alfahari da ku,” in ji Gwamna.