Wani mutum da ake zargi da kasancewa memba na wata fitacciyar kungiyar masu garkuwa da mutane, mai suna Chumo Alhaji daga garin Babanla, ya rasu a hannun ‘yan sanda a Jihar Kwara bayan fama da yawan faduwar warwas.
Majiyoyi sun shaida wa Zagazola Makama cewa a ranar 12 ga Afrilu, 2025, da misalin karfe 10:00 na safe, Alhaji wanda aka kama bisa zargin shirin garkuwa da wasu fitattun mutane a Ajase Ipo — ciki har da Shehu Garba, Sarkin Fulani na Ajase Ipo, da dan kasuwa Alhaji Ali Garba — ya fara faduwar warwas, inda aka garzaya da shi asibitin ‘yan sanda domin kulawa.
An bashi kulawa bisa zargin faduwar warwas ta rashin lafiya (epilepsy), kafin daga bisani a sallame shi.
Sai dai da safiyar washegari, 13 ga Afrilu, Alhaji ya sake samun wani harin warwas kuma aka sake kai shi asibiti, amma duk da kokarin likitoci, ya rasu nan take.
An mayar da gawarsa zuwa Asibitin Koyarwa na Oke Oyi domin gudanar da binciken gawar (autopsy), yayin da hukumomi ke ci gaba da bincike.