Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiTambuwal, El-Rufai Sun Yiwa Gwamna Radda Ta'aziyyar Rasuwar Mahaifiyarsa

Tambuwal, El-Rufai Sun Yiwa Gwamna Radda Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifiyarsa

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya karɓi baƙuncin tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato kuma Sanatan da ke wakiltar Sakkwato ta Kudu, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, waɗanda suka kai masa ziyarar ta’aziyya kan rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Safara’u Umaru Barebari.

Yayin ziyarar da suka kai a fadar gwamnatin jihar da ke Katsina, Sanata Tambuwal ya bayyana ta’aziyyarsa da cewa, “Na dawo daga Saudiyya ‘yan kwanaki da suka gabata, kuma na ga wajibi ne in zo da kaina, a madadina da na iyalina, domin yin ta’aziyya kan wannan babban rashi da ba za a iya maye gurbinsa ba. Rashi mahaifiya abu ne mai nauyi, sai wanda ya fuskanta ne kadai zai iya gane irin radadin sa.”

Sanata Tambuwal ya yabawa marigayiyar da cewa, “Ta rayu rayuwa mai kyau sosai,” sannan ya roƙi Allah da cewa, “Allah ya karɓi ayyukan alkhairinta, ya ba ta mutuwa cikin ƙaunarsa ba tare da jarabawa ba, ya ba ku haƙuri da danginta gaba ɗaya, har da al’ummar Jihar Katsina.”

A nasa jawabin, Malam Nasir El-Rufai ya ce ya samu labarin rasuwar ne a lokacin da yake Japan yana azumin Ramadan, “Na samu labarin wannan babban rashi a yayin da nake Japan. Duk da bambancin lokaci na awa takwas, na yi ƙoƙarin na kira in yi ta’aziyya, amma wasu dalilai sun hana hakan a lokacin.”

El-Rufai ya jaddada muhimmancin ziyararsa da cewa, “Na nace sai na zo Katsina, domin nan ne gida, inda dangi da abokai da kuma mutanen da mahaifiyarka ke ƙauna suke, nan ne za a samu ta’aziyya ta gaskiya.”

Ya bayyana Gwamna Radda a matsayin wanda Allah ya yi wa ni’ima ta musamman, kasancewar mahaifiyarsa ta ga nasarar ɗansa har ya zama gwamna, kuma tana yi masa addu’a a tsawon rayuwarta. “Wannan ni’ima ce ta Allah,” in ji shi.

Tsohon Gwamnan Kaduna ya yaba da shugabancin Gwamna Radda, inda ya ce, “Kai ne ɗaya daga cikin ‘yan gwamnonin da aka zaɓa a 2023 da ke nuna gaskiya da sadaukarwa. Kokarinka wajen ci gaban Katsina da Najeriya duk da ƙalubalen siyasa abin a yaba ne.”

A madadin Gwamna Radda, Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Faruk Lawal Jobe, ya nuna godiya ga ziyarar.

“Muna matuƙar godiya gare ku da tawagarku da kuka ga dacewar zuwa da safe domin yi mana ta’aziyya kan rasuwar mahaifiyarmu. Wannan babban abu ne da muka yi matuƙar yaba masa,” in ji Jobe.

Ya ƙara da cewa, “A madadin gwamnatin Jihar Katsina, dangin gwamnanmu da kuma al’ummar Katsina, muna mai tabbatar muku da godiya da fatan alheri. Kuma kamar yadda muke ci gaba da addu’a, za mu ci gaba da roƙon Allah Ya jikan ta, da sauran waɗanda suka rigamu gidan gaskiya.”

Tsoffin gwamnonin sun hadu da Ministan Gidaje da Ci gaban Birane, Arc. Ahmed Dangiwa; Sanatan Katsina ta Kudu, Sanata Dandutse Mohammed Muntari; Sanatan Katsina ta Arewa, Sanata Nasiru Sani Zangon Daura; Sanatan Katsina ta Tsakiya, Sanata Abdulaziz Musa Yar’adua; tsohon Sanata mai wakiltar Katsina ta Tsakiya, Sanata Kabir Barkiya da kuma ‘yan Majalisar Tarayya.

Ibrahim Kaula Mohammed
Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan Jihar Katsina
14 ga Afrilu, 2025

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments