A cikin wata gagarumar nasara kan miyagun kwayoyi, Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta cafke wata karamar mota dauke da bales shida na kwayar Tramadol da ake zargi, wanda kudinsu ya haura naira miliyan 150, inda aka boye su a karkashin buhunan siminti.
An gudanar da samamen ne a kauyen Alharini da ke karamar hukumar Ungogo, bayan samun sahihan bayanan sirri daga masu ruwa da tsaki. Bayan cikakken bincike da aka gudanar, jami’an suka gano kwayoyin da aka lulube da siminti a cikin motar.
An kama mutum biyu da ake zargi da hannu a lamarin – Imrana Rabiu daga garin Bene a Jihar Kebbi da Muntari Shuaibu daga Kofar Gabas a karamar hukumar Babura ta Jihar Jigawa.
Majiyoyin ‘yan sanda sun bayyana cewa wannan samame na daga cikin kokarin rundunar na ci gaba da yaki da safarar miyagun kwayoyi da sauran laifuka a jihar, tare da hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro.