Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiGwamna Radda Ya Umurci Sabbin Shugabannin Kananan Hukumomi Su Tattala Kudasen Al'...

Gwamna Radda Ya Umurci Sabbin Shugabannin Kananan Hukumomi Su Tattala Kudasen Al’ umma Yanda Ya Kamata

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya ja kunnen sabbin shugabannin kananan hukumomi guda 34 da aka rantsar a yau cewa su tabbatar da amfani da kudaden jama’a cikin gaskiya da rikon amana, tare da bai wa ayyukan da ke da tasiri kai tsaye ga rayuwar al’umma fifiko.

An gudanar da bikin rantsarwar tarihi a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke birnin Katsina, inda babban alkalin jihar, Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar, ya jagoranci rantsarwar.

A yayin jawabin sa, Gwamna Radda ya jaddada muhimmancin adalci da gaskiya wajen tafiyar da harkokin mulki a matakin ƙananan hukumomi.

“Ina kira gare ku da ku gudanar da ayyukanku cikin gaskiya, gaskatawa, da rikon amana. Ayyukan gwamnati ba don amfanin kanku ba ne, sai don alheri ga jama’a. Kowane kobo da aka ware wa majalisunku dole ne a yi amfani da shi don ayyukan da za su inganta rayuwar al’umma,” in ji Gwamnan.

Gwamna Radda ya bayyana wannan rana a matsayin tarihi a Katsina, kasancewar wannan ne karo na farko da aka samu mika mulki daga shugabannin da aka zaba ta hanyar dimokuraɗiyya zuwa wasu sabbi da aka zaba ta sahihin zabe.

Ya ce wannan mataki sabon babi ne a tarihin mulkin ƙananan hukumomi a Katsina.

“Ku ne shugabannin matakin farko da ke da alhakin kawo cigaba, tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a cikin al’ummomin ku. Jama’a na da manyan fata a kanku, saboda ku ne ke da kusanci da su fiye da kowa a gwamnati,” in ji shi.

Gwamna Radda ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa za ta aiwatar da cikakken ‘yancin ƙananan hukumomi a faɗin ƙananan hukumomi 34 na jihar.

Ya ƙara da cewa an kafa sabon sashe a ma’aikatar kula da ƙananan hukumomi da harkokin masarautu wanda zai kasance ƙarƙashin mai ba da shawara na musamman da zai kula da kula da duba-duba domin inganta aiki da kuma ingantaccen amfani da albarkatu a ƙananan hukumomi.

Ya bayyana shiyyoyin aiki guda shida da ya ke so shugabannin ƙananan hukumomi su mayar da hankali a kai: Ilimi da ƙarfin matasa, kiwon lafiya, inganta noma, tsaro da zaman lafiya, gine-gine da kuma kula da muhallin da dorewar cigaba.

Gwamnan ya ja kunnen cewa, “Ba za a lamunci rashawa, sakaci da gazawa ba a karkashin jagoranci na,” tare da ba da tabbacin goyon bayan gwamnati ga shugabannin kananan hukumomi ta fuskar shawarwari, taimakon fasaha da kuma kuɗaɗe.

Shi ma da ya ke jawabi a wajen taron, Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yi kira ga sabbin shugabannin da su kasance masu gaskiya da rikon amana a cikin ayyukansu.

“Bisa jagoranci mai hangen nesa na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, mun samu gagarumar nasara wajen sauya mafarki zuwa gaskiya. Wannan gagarumar halarta da kuka gani yau ba abin mamaki ba ne. Nasarorin Shugaban ƙasa sun samo asali ne daga gaskiya da rikon amana a harkar siyasa,” in ji Dr. Ganduje.

Ya jinjina wa jajircewar shugabannin kananan hukumomi, yana mai cewa, “A madadin shugabancin jam’iyyar APC, muna murnar irin himma da jajircewarku. Mun fahimci muhimmancin jagoranci wajen kawo cigaba a rayuwar jama’a.”

“Ina magana da ku ba kawai a matsayin shugaban jam’iyya ba, amma a matsayin wanda ya taɓa rike irin wannan matsayi – na kasance kansila, shugaban ƙaramar hukuma, sannan na zama gwamna. Na san irin ƙalubalen da ke gaban ku,” in ji Ganduje.

Game da ‘yancin ƙananan hukumomi, Ganduje ya ja kunnen cewa, “’Yanci ba yana nufin ware kai ba ne. Ba yana nufin ku bayyana ne kawai lokacin da aka raba kuɗin gwamnatin tarayya ba. Ba kuma yana nufin fifita amfanin kai sama da jama’a ba ne.”

Taron rantsarwar ya samu halartar Mataimakin Gwamna Malam Faruk Lawal Jobe, Kakakin Majalisar Dokokin Jiha Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura, Sanatoci da ‘Yan Majalisar Tarayya daga Katsina, Shugaban Ma’aikatan Gwamna Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir, Ko’odinetan NEPAD Hon. Abdullahi Jabiru Tsauri, Sarakunan gargajiya da kuma al’ummar kananan hukumomi 34 na jihar.

Ibrahim Kaula Mohammed
Sakataren Yaɗa Labarai

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments