A cikin wani mummunan hari da aka kai da asuba, wasu ‘yan bindiga sun kutsa garin Tungar Dada da ke yankin Moriki a karamar hukumar Zurmi ta Jihar Sokoto, inda suka kashe mutum guda tare da sace wasu mutum 50, a ranar 13 ga Afrilu, 2025.
Majiyoyin leken asiri sun shaida wa Zagazola Makama cewa harin ya faru ne da misalin karfe 4:00 na asuba, lokacin da ‘yan bindigar suka budewa mazauna garin wuta ba tare da wani gargadi ba, kafin su tafi da mutane da dama zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Hukumomin tsaro sun tabbatar da mutuwar ɗaya daga cikin mazauna garin, kuma sun fara gudanar da bincike da kuma farautar ‘yan ta’addan domin ceto mutanen da aka sace da kuma hukunta masu laifin.