Sunday, April 27, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabarai‘Yan Sanda Sun Fara Bincike Kan DPO da Ake Zargi da Karɓar...

‘Yan Sanda Sun Fara Bincike Kan DPO da Ake Zargi da Karɓar Na-Goro a Ondo

Daga Abdullahi Inuwa

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Ondo ta fara bincike kan zargin karɓar kuɗin goro da aka yi wa shugaban sashen ‘yan sanda na Igbara-Oke da ke ƙaramar hukumar Ifedore, CSP Ganiyu Dauda.

Roving Reporters sun ruwaito cewa mazauna garin sun gudanar da zanga-zanga a ranar Juma’a suna zargin DPO da wasu jami’an sashen da karɓar kuɗi daga hannun jama’a ba bisa ka’ida ba. Masu zanga-zangar sun toshe babban titin da ke shiga garin, suna rike da rassan itatuwa domin nuna fushinsu.

Da yake mayar da martani, mai magana da yawun rundunar, DSP Olushola Ayanlade, ya ce rundunar ta fara bincike kan zargin da ake yi wa DPO.

Ya bukaci duk wanda ke da cikakken bayani ko hujja kan zargin karɓar kuɗin goro da a ke yi wa DPO da ya mika wa rundunar domin a gudanar da adalci.

“Rundunar ta ƙaddamar da bincike kan abin da ya faru da kuma zargin karɓar kuɗin goro. Ko da yake, har yanzu babu wanda ya fito ya shigar da ƙara kai tsaye kan DPO. Idan akwai wanda ke da tabbatacciyar hujja, to ya zo da ita,” in ji shi.

“Za mu sanar da jama’a sakamakon binciken da muka gudanar. Muna kira ga al’ummar jihar da su kasance masu bin doka da oda,” ya ƙara da cewa.

Ayanlade ya danganta zanga-zangar da wani rashin fahimta tsakanin ‘yan kungiyar direbobi da wasu ‘yan sanda dangane da janyar wata mota da ta yi haɗari zuwa harabar sashen ‘yan sanda na Igbara-Oke.

Ya ce an warware matsalar ne daga baya ta hannun shugaban ƙaramar hukumar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments