Wani mamba na kungiyar tsaro ta sa-kai, Mika Ahmed mai shekaru 30, ya rasa ransa a ranar 10 ga Afrilu, 2025, sakamakon harbin bindiga da ya rutsa da shi a yayin da suke bin diddigin wasu ‘yan bindiga a Karamar Hukumar Kankara.
Majiyoyin leƙen asiri sun bayyana cewa ‘yan sa-kai na bibiyar wasu ‘yan bindiga ne da suka tsere daga wani samamen soji a kauyen Bakai, inda suka tafi da manyan dabbobi masu yawa da suka sace. Amma a kusa da kauyen Yan Dorowa, sai suka fuskanci kwanton bauna.
A lokacin harin, Ahmed ya samu harbin bindiga a kirjinsa. An garzaya da shi Asibitin Gwamnati na Kankara, amma daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa.
Hukumomi sun tabbatar da cewa za su ƙara zage damtse wajen cafke ‘yan bindigar da suka tsere, waɗanda ake zargi da hannu a wasu hare-hare da dama da suka faru a yankin baya-bayan nan.
Sojoji da ‘yan sanda na ci gaba da sintiri da bincike domin kamo masu laifi da dawo da shanun da aka sace.